UNDP TA YABA WA GWAMNA LAWAL, TA CE GWAMNATIN ZAMFARA TA ZAMA ABIN KOYI GA SAURAN JIHOHI WAJEN TALLAFA WA AL'UMMA

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes24042025_053507_IMG-20250424-WA0057.jpg



Hukumar Raya Ƙasashe ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNDP) ta yaba wa Gwamna Dauda Lawal bisa jajircewarsa wajen ba da tallafin da zai amfani al’ummar jihar Zamfara.

A ranar Laraba ne hukumar UNDP ta ƙaddamar da Cibiyar Magance Ƙalubalen Ci Gaba a Yankin Arewa maso Yamma 'Northwest Prevention Facility Project' a ɗakin taro na Garba Nadama da ke sakatariyar jihar, Gusau.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa aikin ya haɗa da raba kayan noman rani ga manoma 300 da aka zabo bisa la’akari da buƙatunsu.

Sanarwar ta ƙara da cewa, ’yan kasuwa 1,000 za su samu jarin fara aiki na Naira 150,000 kowannensu, da nufin sauya akalar kasuwancin su zuwa sana’o’i na zamani a faɗin Jihar Zamfara.

A nasa jawabin, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada cewa bayan hawansa mulki, gwamnatinsa ta bullo da shirye-shiryen ƙarfafawa da dama tare da samar da damarmaki don cimma manufofinsa na ceto.

“Waɗannan tsare-tsare ba wani kebantaccen abu ba ne, wani ɓangare ne na babban burinmu wajen samar da jihar Zamfara mai albarka don haɗa abokan hulɗa don magance ɗimbim matsalolin zamantakewa da tattalin arziki.

“Yawancin tsare-tsare na rage raɗaɗin talauci da wannan gwamnati ta bullo da su sun yi tasiri ga rayuwar dubban ‘yan jihar, ƙudirin gwamnatinmu na kawar da raɗaɗin talauci yana haifar da ɗa mai ido. Za mu ci gaba da yin haɗin gwiwa tare da UNDP da sauran ƙungiyoyin masu ba da tallafi don samar da ɗorewar hanyoyi don fitar da mutanenmu daga ƙangin talauci.

“Tun da aka fara wannan shirin na bayyana cewa akwai tsari wajen zabi na gaskiya na waɗanda za su ci gajiyar shirin, don haka an zabo waɗanda suka amfana daga garuruwa da ƙauyuka kamar Sankalawa, Furfuri, Karal, Gusau, da Bungudu.

“Ina yawan nanata cewa ƙarfafa tattalin arziki dole ne ya kasance cikin haɗin kai a ƙarƙashin mu, ba tare da barin al’umma a baya ba, shi ya sa na dage wajen ganin an rarraba damarmaki cikin adalci a dukkan ƙananan hukumomin.

"Hakazalika, an gudanar da shirye-shiryen horarwa ga duk waɗanda suka ci gajiyar noman rani. Mun yi imani da cewa samar da albarkatu ba tare da ilimin yadda za a yi amfani da su ba, zai iya iyakance tasirin da shirin ke son cimma."

Gwamna Lawal ya kuma miƙa godiyarsa ga Hukumar Raya Ƙasashe ta Majalisar Ɗinkin Duniya kan yadda suka amince da manufofin gwamnatinsa na ci gaba. “Ga waɗanda suka ci gajiyar, ina ba ku umarni da ku yi amfani da waɗannan albarkatun bisa ga gaskiya, kar ku ba ni kunya a kan yardar da nake da ita akan ku.

“Da waɗannan kalamai, abin farin ciki ne na a hukumance na ƙaddamar da rabon kayayyakin noman rani ga masu cin gajiyar 300 tare da raba jarin fara aikin na N150,000.00 ga ‘yan kasuwa 1,000.”

Tun da farko, shugaban ofishin UNDP na Arewa maso Yammacin Nijeriya, Ashraf Usman, ya bayyana cewa tasiri, sha’awa, da azamar gwamnatin jihar Zamfara a bayyane yake ga kowa da kowa, wanda ke da matuƙar muhimmanci ga haɗin gwiwar.

“Na gode Mai girma Gwamna, waɗannan su ne dalilan da suka sa muka zo nan, ina taya ku murna da goyon bayan ɗimbin jama’a, na gode da irin misalin da ka ke bai wa sauran gwamnatocin jihohi wajen samar wa al'umma tallafi. Na gode da irin jagorancin ka.”

Follow Us