TATSUNIYA: Labarin Samarin Barayi Uku

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes13042025_195331_FB_IMG_1744573855822.jpg


Akwai wani gari mai suna Komayya, wanda yake a yammacin Dajin Dila, kusa da Koramar Kada. A cikin wannan gari, akwai wasu samari guda uku. Na farko ana kiransa Baka Asara, na biyu Barna, sannan na uku Wayo.

Wannan samari ba su da sana’a ko aikin kirki. Abin da suka ƙware a kai shi ne shiga gonakin mutane suna tono rogo ko girbin dawa da masara da gugar su a kasuwa domin su sayar. Wannan ta’asa ta yi yawa har ta ishi mutanen gari. Daga karshe sai aka kafa doka ta musamman don kamo barayin.

Da suka fahimci cewa an kafa doka a garin, sai Wayo ya ba su shawarar su bar garin su je wani gari da ba a san su ba, su nemi abin yi. Sauran biyun suka amince da shawarar, suka bar garinsu suka nufi wani gari.

A wannan sabon gari, suka kwashe shekaru bakwai suna fama da aiki da neman kuɗi, har suka tara kuɗin da suka cika asusu. Da suka ga sun tara isasshen dukiya, sai suka yanke shawarar komawa garinsu. A ranar tafiyarsu, suka kama hanya, Allah kuma ya kai su gida lafiya.

Da suka iso, ba su shiga cikin gari ba sai suka iske wata tsohuwa tana wanke-wanke. Sai suka ba ta ajiyar kuɗinsu, tare da sharadin cewa ba za ta ba kowa daga cikinsu ba sai idan dukkaninsu uku sun zo tare. Tsohuwa ta amince, ta ce:
"To, ku da kuɗinku, kamar yadda kuka ce haka za a yi."

Da suka shiga wanka kuma suka tube kaya, sai suka tuna ba su da sabulu. Sai suka tura Wayo ya je ya karbo sabulu wurin tsohuwa. Da ya isa, sai tsohuwar ta ce ba za ta ba shi ba, domin ba dukkaninsu ne suka zo tare ba.

Wayo ya koma ya sanar da abokansa. Suka yanke shawarar komawa gaba ɗaya. Da suka isa suka ce:
"Mun zo gaba ɗaya, ki ba mu sabulu."

Sai tsohuwa ta ce:
"Sabulu kuma? Kun ce kuɗi zan ba ku idan kun zo gaba ɗaya, amma yanzu kuna tambaya sabulu?"

Daga nan sai suka fusata suka ce dole sai ta ba su Wayo, ko ta nemo shi su karɓi kuɗinsu. Tsohuwa ta ki, suka garzaya kotu wurin alkali. Alkali ya tambayi tsohuwa, ita kuma ta ba da cikakken bayani. Sai alkali ya yanke hukunci cewa cikin kwana uku, tsohuwa ta nemo musu kuɗinsu.

Tsohuwa ta tafi tana kuka. A hanya sai ta haɗu da wani mutum, ya tambaye ta me ke damunta. Ta bayyana masa duk abin da ya faru. Bayan ta gama, sai mutumin ya ce:
"Abin da ya faru da ke, da sauƙi ne."

Tsohuwa ta ce:
"Ta yaya?"

Mutumin ya ce:
"Ki koma wurin alkali ki ce kin samu kuɗin, amma ba za ki ba su ba sai sun zo gaba ɗaya."

Tsohuwa ta gode, washegari ta koma kotu, ta bayyana yadda aka ce da ita. Alkali ya ce:
"Daidai ne. Samari, sai kun samo abokinku ku zo gaba ɗaya kafin a ba ku kuɗin ku."

Samari suka tafi cikin ɓacin rai, tsohuwa kuma ta koma gida da murna.

Shi kuwa Wayo, yana tafiya har rana ta fadi, sai ya yanke shawarar bin wata gajeriyar hanya ta cikin wata gona da suke sata a da. Bai san cewa masu gonar na fakon barayi ba. Da ya shiga, sai suka auka masa. Yana ganin su, ya zaci abokansa ne suka biyo shi. Sai ya zura da gudu, har ya zubar da jakar kuɗin. Bai ma shiga gari ba.

Masu gonar suka kwashi kuɗin, suka raba tsakaninsu ba tare da fargaba ba. Daga baya, suka lura kuɗin sun yi daidai da wanda aka ce an sace rogo da masara da dawa da waken da aka sayar. Suka ce wannan sakamako ne daga Allah.

Daga cikin barayin gonar, biyu suka sayi shanun turka, ɗaya kuma ya faɗa gona. Har yau suna cin duniyarsu lafiya.

Kurunkus!

Darussan da Labarin Yake Koyarwa:

1. Ba a ci amana a kwana lafiya.
2. Ba da umarni a duƙunkune ba tare da bayani ba, na iya janyo matsala.
3. Ko da kai wayo ne, akwai wanda ya fi ka.
4. Wayo a kan rashin gaskiya, wauta ne.
5. Kowa ya tada zaune, bakinsa.
6. Dubu ta cika.

Daga littafin Taskar Tatsuniyoyi Na Dakta Bukar Usman

Follow Us