Gwamna Zulum Ya Umarci A Hukunta Mutumin da Aka Gani a Bidiyo Yana Cin Zarafin Yaro Karami

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes13042025_145024_FB_IMG_1744555531128.jpg

Maryam Jamilu Gambo | Katsina Times 

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayar da umarnin a gaggauta gurfanar da wani mutum mai suna Bukar Modu, wanda aka nuno a bidiyo yana cin zarafin wani yaro ƙarami, Bashir Gaji.

An kama Bukar Modu ne a daren Asabar a unguwar Umarari cikin Maiduguri, bisa umarnin Gwamna Zulum. Gwamnan ya bayar da wannan umarni ne ranar Lahadi yayin da ya gana da yaron Bashir Gaji a fadar gwamnati.

Bidiyon da ya karade kafafen sada zumunta ya tayar da ƙura, inda ya bayyana irin cin zarafin da yara ke fuskanta da kuma buƙatar ɗaukar mataki cikin gaggawa daga hukumomin tsaro da na shari'a.

Gwamna Zulum ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci duk wani nau’in cin zarafin yara ko ƙananan yara ba, kuma ya bukaci a tabbatar da cewa wanda ake zargi ya fuskanci hukunci.

“Wannan aika-aika ya ci karo da dabi’un mu, kuma cin amana ne ga nauyin da ke kan mu na kula da yara da dalibai. Ba za mu bar irin wannan cin zarafi ya ci gaba ba. Ina umartar hukumomin da su gaggauta ɗaukar mataki domin tabbatar da adalci. Yaranmu na da haƙƙin rayuwa cikin tsaro da samun tarbiyya,” in ji Gwamna Zulum.

Haka kuma, ya umarci Ma’aikatar Harkokin Mata da Ci gaban Jama’a da ta tsara shirye-shiryen wayar da kan al’umma, domin ilmantar da iyaye da malamai kan hanyoyin da suka dace na gyara tarbiyyar yara ba tare da cin zarafinsu ba.

A wani bangare, Gwamna Zulum ya gana da ƙaramin yaron Bashir Gaji, inda ya bayyana cewa gwamnati za ta samar wa iyayen sa da gidan zama mai cikakken kayan more rayuwa, tare da tallafin karatu har zuwa matakin da ya ke bukata.

Iyalan yaron na zaune ne a sansanin 'yan gudun hijira da ke Monguno, bayan 'yan Boko Haram sun kashe mahaifinsa.

Follow Us