Rundunar ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayya Abuja ta shiga farautar wasu da ake zargin barayi ne da sace wata motar aiki mallakin Ma’aikatar Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro (ONSA) yayin da ma’aikacin ke Sallar Juma’a.
Rahotannin sirri da jaridar Zagazola Makama ta samu sun nuna cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:05 na rana a ranar juma'a, 11 ga watan Afrilu, inda ma’aikacin ya ajiye motar Hilux baka kusa da AMAC a yankin Area 10 domin gudanar da Sallar Juma’a.
Bayan ya kammala salla, ya dawo ya tarar da motar ta bace babu alamarta, wanda hakan ya nuna an sace ta.
Majiyoyi sun bayyana cewa an sanar da lamarin ga ofishin ‘yan sanda na Garki da misalin karfe 2:00 na rana, lamarin da ya sa rundunar ta hanzarta baza jami’anta domin gudanar da bincike da kuma tsaurara binciken ababen hawa a dukkan hanyoyin shiga da fita daga birnin.
Rundunar ta bayyana cewa tana ci gaba da zurfafa bincike don cafke wadanda ake zargin da kuma dawo da motar da aka sace.
Lamarin ya sake sanya fargaba kan yadda rashin tsaro ke yawaita har a manyan wurare da ake zaton amintattu ne kamar Area 10 a Abuja. A lokaci guda, yana nuna irin barazanar da ke fuskantar ma’aikatan gwamnati, musamman ma masu rike da muhimman mukamai ko bayanan sirri. Wannan na iya zamowa wani abin kara kaimi ga hukumomin tsaro da su kara zage damtse wajen tsare kadarorin gwamnati da kuma tabbatar da cewa ba a yi sakaci da batun tsaro, ko a lokutan ibada ba.