Daga: Muhammad Ali Hafizy, Katsina Times
A cikin yanayin alhini da tunawa da rayuwar marigayiya, Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kurfi da Dutsinma, Hon. Aminu Balele (Dan Arewa), ya jagoranci addu’a ta musamman ga mahaifiyar Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda — Hajiya Safara’u Umar Bare-bari — wadda ta rasu kwana goma sha bakwai da suka gabata.
Taron wanda ya gudana a ranar Juma’a, 11 ga Afrilu, a dakin taro na Kwalejin Ilimi da Fasaha da ke Dutsinma, ya tattaro shugabanni, malamai, dattijai, matasa da mambobin al’umma, inda aka gudanar da addu’o’i da sharhi kan rayuwar marigayiyar da ta rayu cikin tsoron Allah da kishin al’umma.
Hon. Balele ya bayyana marigayiyar a matsayin uwa mai kawaici da sadaukarwa ga al’umma. Ya ce: "Hajiya Safara’u ginshiƙi ce ga addini da al’umma, kuma rayuwarta ta kasance abar koyi ga mata da maza. Rashinta babban gibi ne mai wuyar cikewa."
Bayan kammala addu’ar, Balele ya sauya yanayin taron zuwa na alheri da cigaba, inda ya raba kwamfutoci da tallafin naira dubu ɗari ga matasa guda 50 da aka zabo daga sassa daban-daban. Wannan mataki na daga cikin tsare-tsaren ci gaba da ya ɗauka domin farfaɗo da sha’awar matasa wajen neman ilimi da ƙwarewar zamani.
A cewarsa, wannan ba shi ne karon farko da ya raba kwamfutoci ba, kuma ba zai zama na ƙarshe ba. "Ina da burin ganin matasanmu sun samu kayan aiki da za su taimaka musu su fuskanci rayuwa cikin nagarta da fasaha," in ji shi. Ya jaddada cewa shirin zai ci gaba a matakai daban-daban domin tallafa wa matasa su samu dogaro da kai da kuma gina rayuwar su cikin kwarewa.
Hon. Balele ya yi amfani da damar wajen jan hankalin matasa da su guji duk wani abu da zai jefa su cikin halaka. Ya ja kunnensu da su zama masu girmama manya da mutunta dokokin al’umma tare da amfani da damar da aka ba su ta hanyar da ta dace.
A wani bangare kuma, Hon. Balele ya gana da tsofaffi da sabbin kansiloli na kananan hukumomi. Ga sabbin kansilolin da ake shirin rantsarwa ranar Litinin 14 ga Afrilu, ya basu shawarwari masu ɗauke da darasi da hangen nesa. Ya bukace su da su zama shugabanni nagari da ke kare muradun al’umma fiye da na kansu.
“Shugabanci amana ce. Kada ku bar matsayi ya ruɗe ku. Al’umma sun zabe ku ne domin taimako, ba domin nuna isa ba,” in ji shi. Ya bai wa kowane kansila sabo gudunmawar naira dubu hamsin domin sauƙaƙa musu a farkon tafiyar su.
Ga tsofaffin kansilolin kuwa, Balele ya yaba da irin ƙoƙarin da suka yi a lokacin da suke ofis. Ba wai kawai ya jinjina musu ba, ya kuma tabbatar musu da cewa zai ci gaba da basu alawus na wata-wata domin nuna godiya da goyon baya, tare da miƙa musu gudunmawar naira dubu ɗari kowanne.
Wannan aiki na Hon. Balele yana ɗaya daga cikin alamomin shugabanci nagari wanda ke haɗa da tausayi, hangen nesa, da ɗaukar nauyin cigaban al’umma. Ta haka ne yake ƙara samun karɓuwa a tsakanin jama'a, musamman matasa da ke bukatar shugabanni masu damuwa da su da makomarsu.
Wannan taro da ayyuka masu ma’ana da Hon. Aminu Balele ya jagoranta sun sake tunatar da mu cewa shugabanci nagari ba wai kawai rike madafa ba ne, sai dai aiki tukuru, kulawa da al’umma, da gina tubalin cigaba daga tushe.