Muhammad Ali Hafizy | Katsina Times
Gwamnatin Jihar Katsina ta karɓi rahoton binciken da kwamitin da ta kafa ya gudanar kan yiwuwar sake buɗe kasuwannin dabbobi da ke garuruwan Batsari da Sheme.
Kwamitin, wanda aka kafa a makonnin da suka gabata, ya ƙunshi wakilai daga hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya, 'yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki. An dora wa kwamitin nauyin nazari da gudanar da bincike kan yiwuwar buɗe kasuwannin da aka dakatar da su a baya saboda dalilai na tsaro.
A ranar Talata, 8 ga watan Afrilu, kwamitin ya kammala aikinsa tare da miƙa rahoton ga Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Barista Abdullahi Garba Faskari, ta hannun wakilinsa, Alhaji Mustapha Zubairu (P.S).
Shugaban kwamitin, wanda ya samu wakilcin Alhaji Lawal Garba Faskari, ya bayyana cewa sun kai ziyara garuruwan Sheme da Batsari, inda suka gudanar da tarurruka da masu ruwa da tsaki tare da samun haɗin kai daga jama'a da shugabannin al'umma.
"Mun fara da garin Batsari, inda muka samu kyakkyawar tarba daga wajen hakimin garin, tare da haɗin kai daga shugabannin al'umma. Haka zalika, a Sheme ma an bamu haɗin kai dari bisa dari wajen gudanar da binciken," in ji shi.
Da yake karɓar rahoton, a madadin sakataren gwamnatin jihar Katsina malam Abdullahi Garba Faskari, Alhaji Mustapha Zubairu ya yaba da kokarin kwamitin, yana mai cewa wannan bincike na da matuƙar muhimmanci ga al'umma. Ya tabbatar da cewa zai miƙa rahoton ga Sakataren Gwamnati domin ɗaukar matakin da ya dace kan yiwuwar buɗe kasuwannin.