Daga Farfesa Abdullah Uba
“Samuwar harshen ƙasa wanda kuma shi ne harshen mulki da koyarwa ita ce ma’unin girma da darajar ƙasa a idanun ƙasashen duniya…wajibi ne Jamhuriyar Nijar da Tarayyar Najerya su himmatu da gaske wajen ɗaga matsayin Hausa zuwa matsayin harshen ƙasa kuma na mulki da koyarwa. Hausa ta riga ta zama harshen ƙasashen duniya. Babu makamanciyarta a Nijar da Najeriya.” (Hambali Jinju, 1990)
***
Ci gaban da aka samu ranar 31 ga Maris 2025 a Ƙasar Nijar na ɗaya daga cikin kirarye-kirayen marigayi, Shaihun Malami Farfesa Muhammadu Hambali Jinju (1934-2013). Farfesa Jinju jigo ne a nazari da kuma ɗaukaka harshen Hausa a Tarayyar Najeriya da kuma Jamhuriyar Nijar.
Ya wallafai littattafai da dama ma su inganci a kan harshen Hausa. Waɗannan sun haɗa da “Asalin hausawa da harshensu” (BUK 1993), “Rayayyen Nahawun Hausa” (NNPC, Northern Nigerian Publishing Co., 1980), “African Traditional Medicine: A Case Study of Hausa Medicinal Plants and Therapy” (Indiana University, 1990), “Islam in Africa: Historico-philosophical perspectives and current problems” (ABU 2001) da dai sauran su.
Kusan duk taron da muka shirya tsakanin marubutan Najeriya da na Nijar, sai Farfesa Hambali ya halarta. Muna shirya tararrakin ne a ƙarƙashin Inuwar marubutan Hausa (ANA Hausa) inda na Kano da kuma na Katsina ke haɗuwa a ɗunguma ko Yamai, ko Maraɗi ko Zinder. Kuma duk a ƙarƙashin jagorancin Ado Ahmad Gidan Dabino, saboda yarda da marubutan Nijar suka yi da shi.
Na fara haɗuwa da shi a taron da muka shirya a cikin Agusta 2008 a Maraɗi tsakanin Marubuta da kuma manazartan ƙasashen biyu. A taron kowa ya jinjina masa a matsayin sa na kakan manazarta harshen Hausa. Bayan rasuwar sa, mun shirya Taron Ƙarawa Juna Sani domin Karrama Marigayi Farfesa Hambail Jinju Ƙungiyar Marubuta da Manazarata Harsunan Gida ta Nijar (ASAUNI) da kuma Ƙungiyar Marubuta Harsunan Gida ta Najeriya (NILWA), 19-21 February 2014, Niamey.
Ni a waje na, bakandaiyar rubutun sa ita ce “Garkuwar Hausa Da Tafarkin Ci Gaba: Kalmomin Kimiyya Da Ilimin Fasaha Na Hausa” (1988, Fisbas, 1992). In dai ba shi ne na farko ba, to yana daga cikin jerin na farko-farko inda a ka yi yunƙurin fassara kalmomin kimiyya da fasaha zuwa Hausa ta kowanne fanni. Wannan gagarumar gudunmowa ce ga ci gaban Hausa a fannin kimiyya da fasaha. Kuma amsar ƙalubale ce ga masu ikirarin babu fassarar waɗansu kalmomin kimiyya da fasaha da Hausa. Ai su ma Turawan ba su suka ƙirƙiri abubuwan ba, suna kawai suka ba su da harsunan su, kuma in dai akwai waɗannan abubuwan a kowacce al’umma to lallai al’ummar na da sunan da za ta ba su. Mawallafin ya tunkari wannan kalubalen daga shafi na 9 zuwa na 22 inda ya yi bayanin hujjojin sa dalla-dalla da Hausa, Turanci da kuma Faransanci.
Idan an tsaya a waɗannan shafukan na hujjoji da ɗaukaka Hausa ma kawai an biya kuɗin littafin. Amma gundarin littafin daga 69 zuwa 342 bayanan kalmomin kimiyya da fasaha ne da Hausa.
Majalisar Ɗinkin Duniya (United Nations) na da harsuna shida waɗanda ta ke muhawara da su. Waɗannan su ne: Arabic, Chinese, English, French, Russian, da Spanish. A littafin sa Hambali Jinju ya ce:
“Wajibi ne mu kare hakkin mu na ƴan Adam domin mu ga Hausa ta shiga Majalisar Ɗinkin Duniya da waɗansu ƙungiyoyin ƙasashen duniya.”
Yanzu dai Nijar ta ɗauki jagorancin matakin farko – ƙaddamar da Hausa a matsayin harshen ƙasa. Matakin gaba shi ne fatan shigar da Hausa Majalisar Ɗinkin Duniya, kamar yadda marigayi Hambali Jinju ya yi fata. Allah Ya sa mu dace.
A ina za a samu wannan littafin? Nan fa daya! Ni dai na sayi nawa a BUK Center for Study of Nigerian Languages a lokacin, ana kuma maganar shekaru fiye da 15. Ban sani ba ko har yanzu suna sayarwa. Amma wataƙila Farfesa Malumfashi na da ƙarin bayani, domin a kamfanin sa a ka yi bugu na biyu na Littafin a 1992. Kar kuma a tambayi “soft copy” ko makamancin haka! Old school ne littafin.
Ga bangon littafin, da kuma hoton marigayi Farfesa Muhammad Hambali Jinju wanda na dauka a Maraɗi a Agust 2008.