Alhaji Shafi’u Duwan Ya zama shugaban Kwamitin Zaben Fitar da Dan Takarar Gwamna na APC a Jihar Anambra

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes04042025_072316_Screenshot_20250404-081900.jpg

Uwar jam’iyyar APC ta kasa ta nada Alhaji Shafi’u Abdu Duwan a matsayin shugaban kwamitin da zai jagoranci zaben fitar da dan takarar gwamna na jam’iyyar a jihar Anambra.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta fitar da jadawalin gudanar da zaben gwamna a jihar Anambra, inda ta bayyana cewa za a gudanar da zabukan fidda gwani a cikin watan Afrilu.

Jam’iyyar APC ta kafa kwamitin "Election Management" wanda ya kunshi mambobi goma sha biyar daga sassa daban-daban na kasar nan, kuma Alhaji Shafi’u Duwan ne aka nada a matsayin shugaban kwamitin.

Haka kuma, an nada Alhaji Abdulmalik Mahmood, tsohon mataimakin gwamnan jihar Bauchi, a matsayin sakataren kwamitin.

Wannan kwamitin karkashin jagorancin Alhaji Shafi’u Duwan shi ne zai tsara da kuma tabbatar da nasarar ayyukan sauran kwamitocin da aka kafa domin gudanar da zabukan fidda gwanin jam’iyyar a jihar Anambra.

Za a gudanar da zaben fidda gwanin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Anambra a ranar Asabar, 5 ga Afrilu, 2025.

Alhaji Shafi’u Duwan dai mai ba Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umar Radda (CON), shawara ne kan al’amuran jam’iyya. Ya taba rike mukamin shugaban karamar hukumar Mani, sannan kuma ya kasance sakataren walwala da jin dadin al’umma na jam’iyyar APC a jihar Katsina.

Duwan na daga cikin fitattun jagororin siyasa daga karamar hukumar Mani, kuma matashi ne mai kuzari, hangen nesa da kuma kwarewa wajen mu’amala da jama’a.

Follow Us