Gwamnoni da Masari Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Hajiya Hauwa Radda A Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes02042025_201448_Screenshot_20250402-211244.jpg

Matar tsohon Shugaban Kasar Najeriya marigayi Malam Umaru Musa Yar'adua, Hajiya Hauwa Umaru Radda, ta karɓi baƙuncin Gwamnan Jihar Sakkwato, Dr. Ahmad Aliyu, da takwaransa na Jihar Yobe, Mai Mala Buni, tare da mai ba Shugaban Kasa shawara kan harkokin siyasa, Alhaji Ibrahim Masari.

Ziyarar ta’aziyyar ta biyo bayan rasuwar mahaifiyarsu, Hajiya Safara’u Umar Radda Barebari, inda gwamnonin da mai ba Shugaban Kasa shawara suka jajanta mata tare da yi wa mamaciyar addu’a, suna roƙon Allah ya gafarta mata, ya sa ta huta, kuma ya ba ta makwanci a Aljanna Firdausi.

A yayin ziyarar, gwamnonin sun jaddada muhimmancin haɗin kai da goyon bayan juna a irin waɗannan lokuta masu cike da jarrabawa. Haka kuma, sun yi kira ga dangin mamaciyar da su kasance masu haƙuri da juriya, suna mai da hankali ga kyawawan halaye da marigayiyar ta bari.

Allah ya jikan Hajiya Safara’u Umar Radda Barebari, ya sanya Aljanna makomarta.

Follow Us