EFCC Ta Gurfanar da Ma’aurata Bisa Zargin Yin Damfarar Naira Miliyan 197 da Sunan Matar Gwamnan Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes13032025_161746_FB_IMG_1741881142686.jpg



Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta gurfanar da wani mutum da matarsa, Baba Sule Abubakar Sadiq da Hafsat Kabir Lawal, tare da wasu mutum biyu, Abdullahi Bala da Ladani Akindele, a gaban Mai Shari’a Amina Bello na Babbar Kotun Jihar Kaduna bisa laifin karɓar kuɗi ta hanyar yaudara, wanke kuɗi da kuma sata da suka kai naira miliyan 197,750,000.

An gurfanar da su a ranar Litinin, 10 ga Maris, 2025 bisa tuhume-tuhume guda shida.

A cewar EFCC, waɗanda ake zargin sun haɗa baki don damfarar jama’a ta hanyoyi daban-daban, ciki har da yin kutse da sunan Uwargidan Gwamnan Jihar Katsina, Fatima Dikko Radda, domin yaudarar mutane da karɓar kuɗi daga hannunsu.

Bayanan bincike sun nuna cewa jami’an Hukumar Tsaro ta DSS ne suka fara kama su kafin daga bisani a miƙa su ga EFCC bayan an gano cewa laifukan nasu sun shafi zamba da aikata laifukan kuɗi.

Daya daga cikin tuhume-tuhumen da ake musu na cewa:

"Kai, Hafsat Kabir Lawal, Baba Sule Abubakar Sadiq, Abdullahi Bala da Ladani Akindele Ayodele, a wani lokaci a watan Disamba 2024 a Kaduna, cikin ikon wannan kotu, da niyyar yaudarar mutane, kun karɓi naira miliyan 89 daga hannun wani Aminu Usman, wanda kuka sa aka biya cikin asusun bankin Taj Bank mai lamba 0009914725 da sunan Abdullahi Bala, bisa ƙaryar cewa kuna da dala $53,300 da za ku sauya da kuɗin Najeriya. Wannan laifi ne da ya saɓa wa Sashe na 1(1) na Dokar Zamba da Sauran Manyan Laifuka na Shekarar 2006.”

Dukkan waɗanda ake tuhuma sun musanta laifin da ake tuhumar su da shi.

Lauyan masu gabatar da ƙara, Bright C. Ogbonna, ya roƙi kotu da ta sanya ranar shari’a tare da bada umarnin a ci gaba da tsare waɗanda ake zargin a gidan gyaran hali.

Sai dai lauyoyin waɗanda ake tuhuma, M.S Katu (SAN), Jazuli Mustapha, da Paul A. Okachi, sun nemi belin abokan huldarsu, amma mai gabatar da ƙara ya ƙi yarda, yana mai cewa takardun neman belin ba su shirya don sauraro ba.

Mai shari’a Amina Bello ta goyi bayan masu gabatar da ƙara, inda ta umarci a tsare su a gidan gyaran hali har zuwa 17 ga Maris, 2025, lokacin da za a saurari buƙatar neman beli.

Binciken EFCC ya nuna cewa Hafsat Kabir Lawal ta kira waɗanda ta damfara tana cewa ita ce ɗaya daga cikin matan Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda. Ta haka ne ta samu naira miliyan 89 daga hannun wani mutum da kuma naira miliyan 108 daga wani dan kasuwa da ke son canjin dala $118,300.

Bincike ya kuma gano cewa mijinta, Sadiq (wanda ake zargi na biyu) ne ya ba ta layukan waya biyu tare da rajista da sunan Fatima Dikko Radda a manhajar True Caller. Daga nan ya tuntuɓi Ladani Akindele, wanda tsohon abokinsa ne a wani banki, don neman lambar shugaban bankin Unity, Hafiz Bashir, wanda daga baya ya samo masa lambar wani mai canji.

A ƙarshe, an gano cewa an biya kuɗin cikin asusun Abdullahi Bala, daga nan kuma aka rarraba wa waɗanda ake zargi, inda suka yi ƙoƙarin ɓoye su ta hanyoyi daban-daban.

Follow Us