— Ya kaddamar da rijiyoyin burtsatse, fitilun solar da shirye-shiryen tallafawa matasa
Akalla mutane 3,000 daga kananan hukumomin Dutsin-Ma da Kurfi a Jihar Katsina sun ci gajiyar tallafin kudi da Hon. Aminu Balele Dan Arewa ya rabawa al’ummar mazabarsa.
Mutane da dama sun samu N50,000 kowannensu, yayin da wasu suka karɓi N30,000 tare da kayan abinci domin rage musu radadin halin tattalin arzikin da ake ciki.
An gudanar da rabon tallafin kai tsaye ga gidajen da suka fi bukata, domin tabbatar da adalci da gaskiya.
Ayyukan Raya Kasa
Baya ga tallafin kudi, Hon. Aminu Balele Dan Arewa ya kaddamar da wasu muhimman ayyuka domin inganta rayuwar al’ummar mazabarsa. Ayyukan sun hada da gina rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana a wurare guda shida a garin Kurfi, kamar haka:
1. Nasarawa, kusa da masallacin GPSS Kurfi
2. Sabuwar Unguwa, kusa da gidan Malam Muhalla
3. Saulawa, kusa da gidan marigayi Alhaji Ali Sarkin Aska
4. Gabacin kasuwa, kusa da Yar Chediya
5. Unguwar Low-Cost, kusa da masallaci
6. Kofar Arewa, kusa da makarantar Shehu
Haka nan, dan majalisar ya fara shirin kafa fitilun solar a yankunan da ke bukata a Dutsin-Ma da Kurfi.
Samar da Ayyukan Yi da Tallafawa Matasa
Domin rage zaman banza tsakanin matasa, Hon. Dan Arewa ya samu guraben aiki guda shida a Hukumar Kula da Gobara (Fire Service) ga matasa daga mazabarsa, inda aikin zai fara daga 4 ga Fabrairu, 2025.
Haka nan ya kaddamar da wasu shirye-shiryen tallafawa matasa, da suka hada da:
Tallafin karatu ga dalibai 300 da ke manyan makarantu na gwamnati, inda kowannensu ya samu N30,000 domin rage radadin cire tallafin man fetur.
Horas da matasa 52 kan fasahar zamani (ICT), inda aka basu kwamfutoci (HP Laptop) masu tsada sama da N350,000 kowanne, tare da N100,000 na kudin horo.
Hon. Dan Arewa yayi kaurin suna wajen gabatar da muhimman kudurori da dokoki da suka hada da:
Kuduri kan bukatar kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga a Dutsin-Ma/Kurfi da makwabta.
Dokar kafa Hukumar Raya Arewa maso Yamma, wadda za ta taimaka wajen farfado da yankunan da rikice-rikicen tsaro suka shafa.
Dokar kafa Hukumar Hunters da Forest Security Service domin kare dazuka daga miyagun laifuka.
Dokar kafa Kwalejin Noma ta Tarayya a Kurfi, Jihar Katsina.
Haka zalika, Dan Arewa ya aiwatar da wasu ayyukan jin kai da suka hada da:
Kafa fitilun solar a Dutsin-Ma da Kurfi
Gina tituna a garuruwan Dutsin-Ma da Kurfi
Biyan albashin limamai, da na’ibai na masallatan Jumu’a tun daga watan Maris 2024
Tallafawa ‘yan banga 50 domin karfafa tsaro a mazabarsa
Bayar da kudin magani ga marasa lafiya da kuma taimakawa gidajen da ambaliya ta shafa
Al’ummar Dutsin-Ma da Kurfi sun nuna jin dadinsu da irin ayyukan da Hon. Aminu Balele Dan Arewa ke gudanarwa domin ci gaban yankinsu.
A nasa bangaren, dan majalisar ya jaddada kudirinsa na ci gaba da aiwatar da ayyukan da za su inganta rayuwar jama’a a mazabarsa.