Shugaban ƙungiyar Dikko Project Movement, Honarabul Musa Yusuf Gafai, ya bayyana cewa sake zaɓen Gwamna Malam Dikko Umaru Radda a shekarar 2027 muhimmin abu ne ga al’ummar Jihar Katsina domin ci gaba da aiwatar da ayyukan ci gaban jama’a.
Hon. Musa Gafai ya yi wannan bayani ne yayin taron da ya gudanar tare da shugabannin ƙungiyar na matakin jiha da shiyyoyi uku, da kuma wasu masu ruwa da tsaki a tafiyar. Ya bayyana cewa ƙungiyar Dikko Project Movement za ta ci gaba da gudanar da gangamin wayar da kai a faɗin jihar domin jaddada muhimmancin sake zaɓen Gwamna Dikko Radda don ci gaba da shimfiɗa ayyukan alkhairi da inganta rayuwar jama’a.
Ya jaddada cewa ƙungiyar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yada manufofi da nasarorin Gwamna Radda domin wayar da kan al’umma game da irin ci gaban da aka samu a jihar Katsina.
Bugu da ƙari, Hon. Gafai ya gode wa shugabanni da mambobin ƙungiyar bisa himmarsu na ci gaba da tallata manufofin gwamnatin Malam Dikko Radda a faɗin jihar.
Taron ya samu halartar shugabannin ƙungiyar daga shiyyoyin Daura, Funtua da Katsina, mataimakin shugaban ƙungiyar na jiha, Engr. Abubakar Ɗanbaba Kwado, da kuma shugabannin tafiyar mata na jihar baki ɗaya.
A ƙarshe, Hon. Musa Gafai ya sake jaddada aniyar ƙungiyar na tabbatar da cewa za su samar da kuri’u 564,000 domin sake zaɓen Gwamna Dikko Radda a zaɓen 2027.