Shaikh Zakzaky: Rayuwa, Ilimi da Tasirin Da’awarsa

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes06032025_120418_FB_IMG_1741262405488.jpg


Saifullahi M. Kabir
14 Sha'aban 1444 (6/3/2023)

Shaikh Ibraheem Zakzaky ya karanci ilimin addini a bangaren Jafariyya karkashin malamai daban-daban. Daga cikinsu akwai Sayyid Tabataba’i, wanda ya koyar da shi tsakanin shekarar 1990 zuwa 1993 a Ghana. Daga shekarar 2000 zuwa 2015, ya ci gaba da karatu a Jamhuriyar Musulunci ta Iran, inda ya yi nazarin littafan Imamiyyah da harshen Larabci karkashin jagorancin malamai kamar su Shaikh Jafarul Hadi, Shaikh Dabasi, Ayatullah Ahmadi, Sayyid Ridawi, Farfesa Dahiri da sauransu.

Shaikh Zakzaky, wanda ke da miliyoyin mabiya, ya halarci tarurrukan addini a kasashe da dama. A rayuwarsa, ya yi aikin Hajji sau takwas kuma ya sauke Umrah sau takwas, yana cika watan Ramadan a Makkah. Haka nan, ya ziyarci wuraren ibada na Ma’asumai (AS) a Iraki, Iran, da Madina a lokuta daban-daban.

A matsayinsa na malami, ya rika koyar da ilimin addini, musamman Tafsirin Alkur’ani da Sharhin Nahjul Balagha, ga jama’a a matakin ‘Aama’. Haka nan, ya koyar da wasu daga cikin manyan almajiransa ilimin Fiqihu, Akhlaq, da sauran fannoni a matakin ‘Khas’.

Da’awarsa ta samu goyon baya daga malamai da masana daga bangarorin Shi’a da Sunnah, har da wadanda ba Musulmi ba.

Matsayinsa a idon jagorori da masana

A ranar 29 ga Disamba, 2015, yayin taron hadin kan Musulmi, Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamene’i, ya siffanta Shaikh Zakzaky da cewa:

“Masani, Muslihi, mai kawo gyara da kokarin hadin kan Musulmi, kuma mumini.”

A ganawarsa da masana adabi da mawaka a ranar 20 ga Yuni, 2016, Ayatullah Khamene’i ya bayyana Shaikh Zakzaky a matsayin:

“Mujahidi, jarumi kuma tsayayyen malami na Nijeriya.”

Haka nan, a lokacin rufe Tattakin Arba’een na 2017 a birnin Accra, Ghana, Shaikh Abubakar Ahmad Jamaluddeen ya ce:

“Shaikh Zakzaky yana cikin manyan malamai na Shi’a a duniya. Ana gallaza masa bisa zalunci, amma idan za ka tambayi duniya menene laifinsa? Za a ce maka babu laifi da ya aikata.”

A wajen taron baje kolin Alkur’ani a birnin Tehran, Iran, a ranar 16 ga Mayu, 2019, Farfesa Hassan Shuja’i Fard, wakilin Shaikh Zakzaky a harkokin kasashen waje, ya ce:

“Tun kimanin shekaru 200 da suka wuce, Shehu Usman bin Fodio ya yi bushara da bayyanar wani mai kira, ya ambaci sunansa da siffofinsa. Kuma a daidai lokacin da aka ambata, Shaikh Zakzaky ya bayyana.”

A ranar 29 ga Disamba, 2015, yayin bikin Maulidin Manzon Allah (S) a Lebanon, Sayyid Hassan Nasrullah, shugaban Hizbullah, ya yaba da juriya da hakurin Shaikh Zakzaky:

“Shaikh Zakzaky yana da wayewa da shugabanci na gaskiya. Duk da irin matsayinsa, dattakarsa ta hana tashin hankalin da ka iya kawo hatsaniya. Wannan hali ne na koyi, abin alfahari ga kasa, kuma ya cancanci girmamawa.”

A ganawarsa da iyalan Shaikh Zakzaky a Iran a ranar 30 ga Disamba, 2019, shugaban mabiya Ahlulbait a Bahrain, Shaikh Issa Qaseem, ya ce:

“Allah ya daukaka ambaton Shaikh Zakzaky a duniya, kuma zai daukaka shi a Lahira.”

Ya kara da cewa:

“Shaikh Zakzaky wata makaranta ce a Najeriya da wajenta. Koyarwarsa tana nuna yadda ake Jihadi a tafarkin Allah, sadaukarwa da sallamawa don neman yardar Allah.”

Goyon bayansa daga wadanda ba Musulmi ba

A yayin da almajiransa suka kai masa gaisuwar Kirsimeti a ranar 20 ga Disamba, 2016, Pasto Methosela Ndoma, shugaban wani babban coci a Abuja, ya ce:

“Shaikh Zakzaky mutum ne da babu kamarsa a Najeriya. Shi ne gwarzon yaki da cin hanci da rashawa. Babu duniya a gabansa, burinsa shi ne shiriyar al’umma.”

Shima Rebaran Philips, shugaban cocin Jama’are a jihar Bauchi, a ranar 12 ga Janairu, 2020, ya ce:

“Ana cewa Musulunci addinin zaman lafiya ne, amma ban yarda ba sai da na hadu da Shaikh Zakzaky. Da Najeriya na da irinsa da yawa, da kasar nan ta zauna cikin salama. El-Zakzaky ‘Super Human Being’ ne!”

Hajiya Naja’atu Mohammed, ‘yar siyasa kuma mai rajin kare hakkin dan Adam, a wata ganawa da matasan Sharifai a ranar 9 ga Yuli, 2016, ta ce:

“Shaikh Zakzaky ne kadai ke damuwa da halin da Najeriya ke ciki, kuma shi ne kadai zai iya kawo adalci.”

Kammalawa

Shaikh Ibraheem Zakzaky ya kasance daya daga cikin fitattun malamai da shugabanni a Nijeriya da ma duniya baki daya. Koyarwarsa ta shafi bangarori da dama, daga ilimin addini zuwa kokarin hadin kan al’umma. Yayin da wasu ke ganin sa a matsayin gwarzo, wasu kuma sun dauke shi a matsayin jagoran sauyi.

Daga Jaridar Almizan, bugu na 1583, domin murnar cikar Shaikh Zakzaky shekaru 72 a duniya.
(Kimanin shekaru biyu da suka gabata)


Follow Us