Mai Turaka, Ya Kaddamar Da Fara Rabon Abinci Ga Mabukata Dubu Daya Kullum a Cikin Watan Ramadan.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes02032025_211837_IMG-20250302-WA0047.jpg

Alhaji Abdul'aziz Mai Turaka, Ya Kaddamar Da Fara Rabon Abinci Ga Mabukata Dubu Daya Kullum a Cikin Watan Ramadan.


Muhammad Ali Hafizy, Katsina Times. 

A ranar Lahadi 02 ga watan Maris 2025, fittaccen dan kasuwar nan, kuma shugaban rukunin gidajen man fetur na  Mai Turaka, Alhaji Abdul'aziz, tare da zaɓaɓɓen shugaban karamar hukumar Katsina, Hon Isa Miqdad Ad Saude, suka kaddamar da rabon abinci ga mabukata mutum dubu daya a kullum a cikin wannan watan na Ramadan.

A yayin kaddamar da fara rabon abincin Mai Turaka ya shaida ma yan jaridu cewa, wannan fara rabon abincin ya fara shi ne a cikin watan Ramadan na shekarar da ta gabata, ganin irin albarkar dake ciki shiya bashi kwarin gwiwar sake rabama mabukata a wannan Ramadan din na wannan shekarar.

Ya kara da cewa rabon abincin, sai kasance  ne a lokacin buda baki za'a raba ma mutane guda dari biyar abincin, sannan a lokacin sahur za'a raba ma mutane dari biyar, idan aka hada baki daya zasu kama adadin mutum dubu daya a kullum.

Mai Turaka ya ja hankalin al'umma masu hali akan ayyukan alkairi a cikin wannan watan, ya shaida cewa ba dole sai ka yi abu mai yawa ba wajen ciyar da mutane ba, ko da abu kadan ne ka mallaka ka bayar dashi sadaka to zaka samu ladar mai yawa.

Follow Us