LHon. Aminu Balele Kurfi Ya Ziyarci DG Budget, Sun Tattauna Kan Ci Gaban Yankinsu

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes28022025_201929_IMG-20250228-WA0109.jpg

Hon. Aminu Balele Kurfi Ya Ziyarci DG Budget Dr. Tanimu Yakubu Kurfi, Sun Tattauna Kan Ci Gaban Dutsinma da Kurfi

Hon. Aminu Balele Kurfi, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Dutsinma da Kurfi a Majalisar Wakilai ta Ƙasa kuma shugaban kwamitin sojojin ƙasa, ya kai ziyara ta musamman ga Darakta Janar na Hukumar Kasafin Kuɗi ta Ƙasa, Dr. Tanimu Yakubu Kurfi.

Ziyarar da aka kai a ofishin DG Budget na da nufin taya Dr. Tanimu Yakubu Kurfi murna kan sanya hannu a kasafin kuɗin shekara ta 2025, wanda ke da matuƙar muhimmanci ga cigaban ƙasa. Bugu da ƙari, sun gudanar da muhimmiyar tattaunawa kan yadda za a inganta cigaban kananan hukumomin Dutsinma da Kurfi, tare da nazarin hanyoyin da za su taimaka wajen tabbatar da aiwatar da muhimman ayyuka masu amfani ga al’ummar yankin.

Hon. Aminu Balele Kurfi ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin bangaren dokoki da bangaren zartarwa domin tabbatar da aiwatar da manyan tsare-tsare da za su inganta rayuwar al’umma, musamman ma a yankin Dutsinma da Kurfi.

Follow Us