Farfaɗo da Ilimin Manya: Hukumar Ilimin Ta Jiha da NMEC Sun Ziyarci Masarautar Daura

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes26022025_203944_FB_IMG_1740602305833.jpg



Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times | 26, Fabrairu 2025

A wani yunkuri na farfaɗo da ilimin manya a jihar Katsina, wata tawaga daga Hukumar Ilimin Manya ta Ƙasa (NMEC) tare da Hukumar Ilimin Jiha ta Katsina sun kai ziyara Masarautar Daura a ranar Laraba, 26 ga Fabrairu, 2025. Tawagar, ƙarƙashin jagorancin Alhaji Yusuf Abdulkadir Aliyu, Koodinetan shiyyar Arewa maso Yamma na NMEC, da Hajiya Bilkisu Muhammad Kaikai, Babbar Daraktar Hukumar Ilimin Jiha ta Katsina, sun kai wannan ziyara ne domin ƙarfafa shirye-shiryen yaki da jahilci tare da raba kayan koyarwa ga makarantu.

Ziyarar ta kuma dace da shirin Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Umar Radda, PhD, wanda ke da nufin farfaɗo da makarantun manya (Mass Education) tare da faɗaɗa shirin zuwa dukkanin gundumomin hakimai da dagatai a cikin ƙananan hukumomi 34 na jihar.

Da yake jawabi yayin ziyarar, Alhaji Yusuf Abdulkadir Aliyu, wanda ke kula da jihohin Katsina, Sokoto, Zamfara, Kebbi, Kano, Jigawa, da Kaduna, ya bayyana cewa aikin hukumar shi ne tsara manufofin ilimin manya tare da tabbatar da cewa an aiwatar da su a matakin jiha da ƙananan hukumomi.

"Ayyukanmu shi ne ƙirƙirar manufofin ilimin manya. Bayan mun tsara su, sai mu tura wa jihohi, su kuma su miƙa wa ƙananan hukumomi don aiwatarwa. Wannan shi ne tsarin da ke bada damar isar da ilimi zuwa mafi nisa na yankunan karkara," in ji shi.

Ita ma a nata ɓangaren, Hajiya Bilkisu Muhammad Kaikai ta jaddada cewa Gwamnatin Jihar Katsina na da ƙudurin magance jahilci da rashin aikin yi, domin wadannan abubuwa ne ke haifar da matsalar tsaro a jihar.

"Gwamna Malam Dikko Umar Radda ya himmantu matuƙa wajen yaƙi da jahilci da rashin aikin yi. Idan aka ilmantar da al’umma tun daga matakin ƙasa, za su fi fahimtar bambancin tsakanin abin da ya dace da wanda bai dace ba. Ba kawai ilimin boko muke mayar da hankali ba, har da ilimin addini da koyar da sana’o’i domin mutane su samu damar dogaro da kansu," in ji ta.

Hajiya Kaikai ta kuma yi kira ga Masarautar Daura da su bada ƙarin goyon baya don samar da cibiyoyin ilimi a gidajen sarakuna da hakimai a fadin jihar Katsina. Haka kuma, ta roƙi ‘yan siyasa da masu hannu da shuni su taimaka da kayan koyar da sana’o’i kamar keken dinki, keken saka, da kayan koyon sana’o’i domin ci gaban shirin.

Da yake mayar da martani, Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Faruq Umar Faruq CON, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga shirin, yana mai cewa masarautar Daura tana da dogon tarihi a fannin yaki da jahilci tun daga shekarar 1955.

"Ni kaina na fara aikin yaƙi da jahilci tun a shekarar 1955. A lokacin ina kula da shirye-shiryen koyar da manya a yankin Daura. Na yi aiki a ƙaramar hukumar Zango a ƙarƙashin Shehu Kafin Dangi, wanda shi ne jami’in Turawan mulkin mallaka da ke kula da yankin Katsina kafin a kafa jihar," in ji shi.

Sarki ya kuma bayyana cewa a baya, malamai masu koyar da manya suna karɓar albashi mai tsoka fiye da sauran ma’aikata.

"A lokacinmu, albashinmu yana da matuƙar daraja. Muna karɓar shilling 18 a kowane wata, wanda ya fi albashin wasu manyan ma’aikata na wancan lokaci. Haka kuma, duk kauyukan masarautar Daura suna da allon karatun yaƙi da jahilci, kuma a lokacin na kafa doka da ta tilasta wa kowa zuwa makarantar manya—wanda bai halarta ba yana fuskantar hukunci," in ji shi.

Sarki ya kawo misali da gasar "Takobin Himma", wanda ake bai wa hakimi mafi himma a yaƙi da jahilci a lokacin bikin Sallar Gani. Ya bayyana cewa mahaifinsa ne ke lashe wannan gasar a kowace shekara, domin ƙoƙarin da ya ke yi a fannin ilimi a masarautar Daura.

A yayin ziyarar, Hajiya Bilkisu Kaikai ta kai ziyara zuwa cibiyoyin ilimin manya da koyon sana’o’i a ƙananan hukumomin Daura da Mashi domin tantance matsalolin da ke fuskantar su.

A Daura, ta duba kalubalen da makarantun ke fuskanta, tare da alkawarin ɗaukar matakin magance su. A Mashi, an gano cewa malaman da ke koyarwa ba su da ginin makaranta na dindindin, inda suke amfani da wurin aro daga ƙaramar hukuma. Sai dai, shugaban ƙaramar hukumar Mashi ya bada fili a harabar sakatariyar ƙaramar hukuma domin a gina cibiyar koyar da ilimin manya ta dindindin.

Daga cikin tawagar da suka halarci wannan ziyarar sun hada da: Alhaji Yusuf Abdulkadir Aliyu (Jami’in NMEC), Malam Jafar Abubakar,
Mr. Tyungu Terseer G, Hajiya Bilkisu , Muhammad Kaikai (Babbar Daraktar Hukumar Ilimin Manya ta Katsina), Hassan Ummaru (DPRS), Murja Ahmad Sa’i, Amina Audu Fari, Bilkisu Abdullahi Yusuf, Binta Balan Gwaggwo
Hadiza Ahmed, Bilkisu Ado Shinkafi, Shafiu Sani, Lawal Taro Abubakar, Ahmad Muhammad
Aminu Muhammad. 

Ziyarar da NMEC da Hukumar Ilimin Manya ta Katsina suka kai Masarautar Daura na nuna matakin da ake ɗauka domin farfaɗo da ilimin manya a jihar Katsina. Tare da haɗin gwiwar masarautu, gwamnati, da al’umma, ana fatan cimma burin ƙarfafa ilimi da sana’o’i, wanda zai taimaka wajen rage jahilci da rashin aikin yi a jihar.

Follow Us