KIWON LAFIYA: Maleriya — Hanyoyin Kamuwa, Alamominta da Matakan Kariya

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes20072025_193923_causes-malaria-1536x1026.jpg


KatsinaTimes Health Desk

Cutar maleriya na daga cikin manyan cututtukan da ke barazana ga lafiyar al’umma, musamman a nahiyar Afirka da kuma Najeriya baki ɗaya. Wannan cuta tana yaduwa ne ta hanyar cizon macen sauro mai ɗauke da ƙwayar cutar Plasmodium, wacce ke shiga jinin mutum ta kuma fara lalata kwayoyin halittar jini.

Hanyoyin da ake kamuwa da Maleriya

Mutum na iya kamuwa da cutar maleriya ta hanyoyi da dama: ga wasu daga cikin su

Cizon macen sauro; da ke ɗauke da kwayar cutar Plasmodium.
Zama a wurare da ke da cunkoson sauro, musamman a lokacin damina ko inda ruwa ke taruwa a bude.
Rashin amfani da kayan kariya, kamar gidan sauro ko magungunan da ke korar ko kashe sauro.
Rashin tsaftar muhalli, wanda ke haifar da sauƙin haifar da sauro a kusa da gida.

Alamomin da ke nuna mutum na dauke da Maleriya

Cutar maleriya na bayyana da wasu alamomi da suka haɗa da:

Zazzabi mai hawa da sauka, wanda yakan zo da tsananin jin sanyi da karkarwa.
Ciwon kai mai tsanani da yawan jin gajiya ko kasala.
Ciwon jiki da tsoka, musamman baya da ƙafafu.
Amai ko ama-ama, wasu lokuta har da gudawa.
Yawan zufa da jin sanyi lokaci guda.
 A wasu lokutan, cutar na iya janyo lalacewar hanta, ƙwaƙwalwa, ko ma mutuwa, idan ba a samu kulawa da gaggawa ba.

Matakan Kariya da Rigakafin Maleriya

Don kaucewa kamuwa da wannan cuta, ana bukatar ɗaukar matakai kamar haka:

1. Amfani da gidan sauro mai feshi da magani (wato LLIN – Long-Lasting Insecticidal Nets), musamman yayin barci.
2. Feshe dakuna da maganin sauro, musamman a lokacin damina.
3. Tsaftace muhalli da kawar da danshin ruwa, wanda ke zama mafakar sauro.
4. Shan maganin rigakafi, musamman ga mata masu juna biyu da kuma yara kanana, kamar yadda cibiyoyin lafiya ke ba da shawara.
5. Gaggauta zuwa asibiti da zarar an fara jin alamomin maleriya, domin a tabbatar da cutar da kuma samun kulawa da wuri.

Maleriya cuta ce da za a iya guje mata idan aka bi hanyoyin kariya da kuma neman magani da wuri. Haka kuma, ya kamata a ci gaba da wayar da kan jama'a, musamman a yankunan karkara, domin rage yawan mace-mace da rashin lafiya sakamakon cutar.

Follow Us