AN ƘARA KARFAFA HADIN GWIWA TSAKANIN FRSC DA KASSAROTA A KATSINA

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes26022025_093832_IMG-20250225-WA0024.jpg



25/02/2025

Daraktan Janar na Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Ababen Hawa da Tsaro ta Jihar Katsina (KASSAROTA), Manjo Garba Yahya Rimi (Rtd), ya karɓi ziyarar ban girma daga Kwanturolan Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC) a Jihar Katsina, CC Aliyu Ma’aji.

A yayin ziyarar, CC Aliyu Ma’aji ya nuna matuƙar godiya bisa kyakkyawar tarbar da aka yi masa tare da tawagarsa. Ya jaddada cewa akwai kyakkyawar dangantaka mai ɗorewa tsakanin FRSC da KASSAROTA, wanda ya samo asali daga haɗin gwiwa a fannoni da dama, ciki har da musayar bayanan sirri, gudanar da ayyukan hadin gwiwa da horarwa.

Shugaban Hukumar Kiyaye Hadurra FRSC a jihar ya bayyana cewa manufar wannan ziyara ita ce ƙara ƙarfafa alakar dake tsakanin hukumomin biyu.
"Mun zo ne don neman haɗin gwiwar ku, da ƙarfafa fahimta tare da tabbatar da ci gaba da yin aiki tare."

Ya ƙara da cewa FRSC za ta ci gaba da yin aiki tare da KASSAROTA wajen kare lafiyar jama’a, tabbatar da tsaro, da kuma kiyaye rayuka da dukiyoyin al’umma.

A nasa jawabin, Daraktan Janar na KASSAROTA, Manjo Garba Yahya Rimi (Rtd), ya nuna farin cikinsa da wannan ziyarar daga Kwanturolan FRSC tare da tawagarsa. Ya jaddada ƙudirin KASSAROTA na ci gaba da inganta kyakkyawar alakar aiki da FRSC a jihar.

Har ila yau, ya bayyana cewa KASSAROTA da FRSC suna gudanar da gagarumin aiki tare a jihar, kuma za a ci gaba da ƙarfafa irin waɗannan ayyuka domin inganta tsaro da kyautata zirga-zirgar ababen hawa.

Daga
Abubakar Marwana Kofar Sauri
Jami'in Hulda Da Jama'a Na Hukumar KASSAROTA a Jihar Katsina

Follow Us