Kamar yadda Tarihin ya nuna Asalin BADAWA ya farone daga Yemen ta Kasar Larabawa. To daga nanne Badawan sukayo Kaura tare da Barebari adai dai karni na goma Sha ukku ( K13). BADAWA sun fara kafa Garin Tagali, acikin karni na Sha ukku (K13). Daga nan suka kafa Garin Dadigar da Gid-Gid, har ya zamana ana yimsu lakabi da Badawan Gid-Gid da Dadigar. Saboda rashin kyakkyawan tsaro da rashin kwanciyar hankali da hare hare, yasa BADAWA suka kafa Garin GORGORAM.
Dalilin Kiran wurin GORGORAM, don kasantuwarsa ta daji Mai Duhu, Mai nisan gaske, wanda yake cike da itatuwa masu sarkakiya da ciyawu iri iri da namun daji barkatai. A shekarar 1825 ne aka zagaye Garin GORGORAM da Ganuwa ta hanyar Taimako daga sauran Badawan Tigali da Katamma da Dumbari da sauransu. Tun daga wannan lokacinne BADAWA suka hade kansu wuri daya a karkashin Jagorancin Lawan Babuje. Har ya zuwa yanzu zuriyar Lawan Babuje suke suke mulkin Kasar Bade, da mikamin Mai Bade.
TASOWAR MASARAUTAR BADE ZUWA GASHUA (1946).
Acikin shekara ta 1946 ne Turawan mulkin Mallaka suka nemi Masarautar Bade dake GORGORAM ta koma GASHUA. A lokacin GASHUA tana karkashin ikon Kanem- Borno, ita kuma GORGORAM tana rike da wani Gari Wacakal kudu da Nguru, kimanin Kilomita shida ko bakwai. To sai akayi canji aka ba Kanem- Borno Wacakal, ita kuma Hedikwatar Bade aka dauko ta daga GORGORAM ata dawo da ita GASHUA acikin shekarar 1946. Wannan dalilin ne yasa har ya zuwa yanzu Masarautar Bade take ansa sunan Sarkin ta da Mai Bade, sannan sunan Karamar Hukumar Bade, Amma Hedikwatar GASHUA.
Lokacin da Badawa suka shigo Garin GASHUA sun tarar da sauran Kabilu a Garin da suka hada da Bare- Bari da Buzaye da Hausawa da Fulani da Ngizim da sauransu. Akwai kuma unguwanni acikin GASHUA da suka hada da Dandal ( Kofar Fada) da Lawan GASHUA da Lawan Hausawa da Barebari da Katuzu da Zango na 1 Dana 2 da Unguwar Kudu da Unguwar Makafi da Sabon Gari da sauransu.
A halin yanzu Garin GASHUA ya tara manyan mutane irinsu:-
1. Mai Martaba Sarkin Bade ( Mai Bade Alhaji Abubakar
Umar Suleiman)
,2. Senetor Ahmed Lawan ( Former Senate President)
3. Engineer Buba Galadima( Political.Activist)
Ta fannin Mawaka akwai su
4. GARBA GASHUA DA SAURANSU.
Alhaji Musa Gambo Kofar soro.