Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times
Yayin da watan Ramadana ke kara kusantowa, masana kimiyyar lafiya sun ja hankalin Musulmi masu azumi kan irin nau’in abinci da yakamata su ci domin kare lafiyarsu, da kuma wanda yakamata su guje wa saboda illa da zai iya haifarwa. Binciken masana ya nuna cewa cin abinci mai gina jiki da kuma gujewa wasu nau’in abinci masu illa yana taimakawa wajen samun kuzari da kiyaye lafiya a lokacin azumi.
Abincin da Mai Azumi Yakamata Ya Ci
Masana sun bada shawarar cewa mai azumi ya fi dacewa da cin abinci mai wadatar sinadaran gina jiki da kuma rike jiki da kuzari. Ga wasu daga ciki:
1. Abinci Mai Yawan Fibr: Irin su gero, alkama, shinkafa mai laushi (brown rice), da wake suna da matukar muhimmanci, saboda suna taimakawa wajen tsawon lokacin jin koshi da kuma hana matsalolin narkewar abinci.
2. 'Ya'yan Itatuwa da Kayan Lambu: Kamar su ayaba, kankana, dabino, lemu, kokwamba, karas, da tumatir suna dauke da sinadaran da ke kara ruwan jiki da kuma kara lafiya.
3. Abinci Mai Wadatar Protein: Kamar su kaza, kwai, nama mara kitse, kifi, da wake suna taimakawa wajen bunkasa garkuwar jiki da kuma ba da kuzari.
4. Ruwan Sha: Yana da matukar muhimmanci a shan isasshen ruwa daga lokacin buda-baki har zuwa sahur don hana bushewar jiki.
5. Madara da Kayayyakin Madara: Kamar su nono, cuku, da yogurt suna da sinadarai masu karfafa kashi da garkuwar jiki.
Abincin da Mai Azumi Yakamata Ya Gujewa
Masana lafiya sun jaddada gujewa wasu nau’in abinci domin hana matsalolin lafiya kamar:
1. Abinci Mai Yawan Kitse da Mai: Kamar su soyayyen abinci irin su waina, doya da kwai, yaji mai yawa, da nama mai kitse, saboda suna iya haddasa ciwon ciki da yawan jin gajiya.
2. Abinci Mai Yawan Sukari: Kamar su lemun kwalba, alewa, cakulan, da sauran kayan zaki masu nauyi, saboda suna haddasa karuwar sukari a jiki da kuma sa gajiya cikin gaggawa.
3. Abinci Mai Yawan Gishiri: Kamar su dambun nama da kwalam, saboda yana iya haddasa bushewar jiki da karancin ruwa.
4. Shan Ruwa Mai Sanyi da Sauri: Yana iya haddasa matsalar narkewar abinci da ciwon ciki.
5. Shan Ruwa Kadan a Budar Baki da Sahur: Rashin shan isasshen ruwa yana iya haddasa bushewar jiki da kuma rage kuzari.
Masana lafiya suna bada shawara ga masu azumi da su rika cin abinci cikin hankali ba tare da cunkushe cikinsu ba. Hakanan, sun bukaci su rika samun isasshen hutu da gujewa wahalar da jiki. Yana da kyau a yi sahur don samun karin kuzari da rana, sannan a yi kokarin samun abinci mai inganci domin kiyaye lafiya a watan mai alfarma.