An Bude Katafaren Masallacin Juma’a a Rukunin Gidajen Asibitin Koyarwa ta Gwamnatin Tarayya a Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes21022025_213148_FB_IMG_1740173423757.jpg



An Nada Babban Limami tare da Shawarwari Kan Hadin Kai da Ci Gaban Addini

Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times | 21 Ga Fabrairu 2025

A ranar Juma’a, 21 ga Fabrairu 2025, an gudanar da walimar bude sabon katafaren Masallacin Juma’a a rukunin gidajen Asibitin Koyarwa na Gwamnatin Tarayya da ke garin Katsina. Taron ya samu halartar manyan shugabanni, sarakuna, da al’ummar gari, inda aka nada babban limamin masallacin tare da jaddada mahimmancin hadin kai da ci gaban addini.

Mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Dakta Abdulmumini Kabir Usman, ya jagoranci taron tare da halartar wakilin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, wanda mai ba shi shawara kan harkokin addini, Alhaji Gambo Agaji, ya wakilta. Haka kuma, Alhaji Dahiru Barau Mangal ya samu wakilcin dan majalisar karamar hukumar Katsina, yayin da shugabannin kananan hukumomin Jibiya da Batsari, ‘yan siyasa, malamai, da sauran manyan baki suka halarta.

A jawabinsa, Mai martaba Sarkin Katsina ya bukaci al’ummar musulmi da su kara karfafa hadin kai da zumunta domin ci gaban addini da zaman lafiya. Bayan haka, ya tabbatar da nadin babban limamin da zai jagoranci sallar Juma’a a masallacin, wanda ke da matukar muhimmanci wajen karfafa ayyukan ibada da wa’azin addini a yankin.

A nasa bangaren, Alhaji Gambo Agaji, a madadin Gwamnan Jihar Katsina, ya yaba da kokarin al’ummar yankin bisa gina wannan katafaren masallaci. Ya ce wannan aiki ne na alheri da zai ci gaba da amfani ga al’umma har abada, tare da bukatar a ci gaba da irin wadannan ayyuka na ci gaban addini da zamantakewa.

Wakilin attajirin dan kasuwa, Alhaji Dahiru Barau Mangal, wato Hon. Ali Abu, ya amsa kiran Mai Martaba Sarkin Katsina tare da bayyana shirinsa na tattaunawa da kwamitin unguwar domin samar da makarantar Islamiyya a kusa da masallacin. Ya ce, “Da yardar Allah, za mu duba hanyoyin da za a bi domin kafa makarantar Islamiyya da za ta taimaka wajen inganta ilimin addinin Musulunci.”

A karshe, Mai Martaba Sarkin Katsina tare da tawagarsa sun bude masallacin tare da gudanar da sallolin nafila raka’a biyu domin neman albarka. Wannan masallaci na daya daga cikin muhimman wuraren ibada da za su taimaka wajen ci gaban al’umma da karfafa addinin Musulunci a Katsina.

Follow Us