'Yan Wasan Katsina Football Academy Sun Shilla Zuwa Qatar Don Gasar Kallon Ƙwazon Ƴan Wasa

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes21022025_184512_IMG-20250221-WA0063.jpg


'Yan wasan Katsina Football Academy sun tashi zuwa Doha, Qatar, domin halartar wata gasa ta ƙallon ƙwazon 'yan wasa da za ta gudana na tsawon mako guda, daga ranar 21 ga Fabrairu, 2025.

'Yan wasan za su baro Kano don wannan tafiyar ta ƙwallon kafa, inda za su fafata da fitattun ƙungiyoyin ƙasar Qatar, ciki har da Al-Rayyan, Al-Dohen, da Al-Sahel.

Daraktan Hukumar Wasanni ta Jihar Katsina, Audu Bello, wanda ya wakilci Kwamishinan Matasa da Wasanni na Jihar, Aliyu Lawal Zakari Shargalle, ya jagoranci bikin bankwana ga tawagar 'yan wasan.

A yayin taron, Bello ya isar da saƙon Kwamishinan, inda ya jaddada muhimmancin da’a, gaskiya, da ɗabi’a mai kyau ga 'yan wasan yayin da suke wakiltar jihar a gasar.

Haka nan, Daraktan Kwallon Kafa na Makarantar, Shamsuddeen Ibrahim, ya nuna kwarin gwiwar cewa za su jagoranci 'yan wasan domin cimma burinsu.

A cikin tawagar, akwai Kwamishinan Matasa da Wasanni na Jihar, Hon. Aliyu Lawal Shargalle, Shugaban Akademi, Ahmed Muhammad, da Shugaban Kwamitin Majalisar Jihar kan Wasanni, Mustapha Sani Bello.

Wannan damar ta biyo bayan sanarwar da Gwamnatin Jihar ta yi a ranar 18 ga Fabrairu, 2025, inda ta bayyana shirinta na daukar nauyin shirin ci gaban wasanni a Africana People Academy da ke Doha.

Gasar na bai wa matasan 'yan wasa daga Katsina dama don nuna basirarsu a idon duniya tare da samun zarafin shiga kungiyoyin ƙwallon ƙafa na ƙasa da ƙasa.

Follow Us