Mun kammala dukkan shirye-shiryen zabukan kananan hukumoni na jihar Katsina,- KTSIEC

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes12022025_185534_FB_IMG_1739386424900.jpg

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar katsina (KTSIEC), Alhaji Lawal Alhassan Faskari ya bayyana cewar sun kammala dukkan shirye-shiryen gudanar da zabukan shugabannin kananan hukumomin jihar wanda za a yi a ranar Asabar 15 ga wannan wata na Fabrairun 2025.

Faskari ya bayyana hakan ne a yayin da yake fira da jaridun KatsinaTimes da Taskar Labarai dandange shirye-shirye zabukan kananan hukumomin a ranar Laraba nan a Ofishinsa.

Ya ce tun da farko a shekarar bara, sun fara gangami tare da bayar da jadawalin zaben ga daukacin jam'iyyu ne, inda bayan kammala zaben fidda gwanin kowace jam'iyya suka fara siyar da Fom din Takara.

"Mun saida Fom sannan muka zo muka tantance su." In ji shi.

"A nan hedikwata an tantance Ciyaman da mataimakinsa, a kananan hukumomi an tantance kansiloli wanda malamin zabe namu da sauran masu taimaka masa suka tantance su."

Dangane shire-shiryen zaben da za a aiwatar a ranar Asabar, Alhaji Lawal Faskari ya ce sun ba wa ma'aikan horo yadda ya kamata, kuma shi kansa a matsayinsa na kwamishinan nan zaben an ba shi nashi horo.

"Mun ba ma'akatan zaben horo sau kusan kashi uku ko hudu. Sannan mu kanmu kwamishinoni, mu ma an ba mu horo kusan kala biyu dangane da wannan zaben.

Don samun shugabbin al'umma nagari a kannan hukumomin, kwamishin ya ce tun da farko sai da suka fara tantance duk wani dantakar kan alaka da shan kwaya.

"Akwai abin da muka bullo da shi a wannan karon na tantance 'yantakara kan ta'ammuli da miyagun kwayoyi, wanda hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi suka aiwatar." In ji shi.

"Mun yi wannan ne domin karamar hukuma ta samu nagartattunn shugabanni wadanda ba su mu'amala da wadannan miyagun kwayoyin. Kuma Alhamdulillahi tantancewar da aka yi ba a samu 'yantakarkarin mu'amala da wannan ba." Ya tabbatar.

 Dangane da tsare-tsare don samun ingantaccen zabe ba tare da tangarda ba, Lawal Faskari ya ce sun zo da sabbin tsare a zabukan.

"Wannan karon ya bambanta da abubuwan da aka yi a shekarun baya, domin wannan karon mun raba kayayyakin zabe (Sensitive materials), sannan mun dauki ma'akata na wucin gadi wadanda za su yi aikin kusan mutum dubu 20,000 kuma mun ba su horo."

"An tanadi kayayyakin zabe wanda ake rabawa in ana gobe zabe, inda kowace hukuma aka yi mata nata tsarin daban."

"Yanzu abin da ya rage mana shi ne raba kayayyakin zabe na ana kwana daya ko biyu yin zabe." Ya sanar.

Haka kuma, kwamishinan ya tabbatar da cewar sun bi dukkan ka'idoji da doka ta tanar game da zaben.

"Tun farko, bisa tsarin doka muka bi. Duk abin da kundin tsarin mulki da kundin tsarin zabe na kasa da na jiha ya ce, su muka bi."

"Na farko sai da muka bada kwanaki dari 365, wanda a doka cewa aka yi a bada kwanaki 360 kamar yadda sashe na 28 na kundin zabe wanda aka yi wa kwaskwarima na 2022, wanda shi kuma sashe na 50 na kundin tsarin ya ce wanda duk bai bi wannan tsarin da aka bayar ba, to ana iya rushe wannan zaben." To gudun wannan ya sa duk ka'idojin da aka fada mun bi su. Domin ko kudin Fom da muka sa, doka ce ta ba mu dama mu sa.

Daga karshe, ya bayyana cewar jam'iyyu biyar kadai ne za su shiga zaben, inda ya ce hukumar zaben ta yi tsari mai kyau kuma gamsasshen wanda zai bada fa'ida tayadda za a aiwatar da zaben sahihi, a tsanake, da kuma tsaro.

Follow Us