Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A rana ta biyu, na ci-gaban da yakin neman zaben Dantakarar kujerar shugaban karamar hukumar Katsina, a karkashin Inuwar jam'iyyar APC Honorabul Isah Miqdad AD Saude, na kara karɓuwa ga mutanen karamar hukumar, a inda yake bi lungu da sako na Birnin Katsina don neman alfarmar jama'a, kamar yadda Al'adar siyasar take.
Isah Miqdad AD Saude Ya ziyarci Mazabun Shinkafi 'A', Shinkafi 'B' da Gabas 1, duk a cikin birnin Katsina, inda al'umma suke tururuwa domin tarbar Dantakarar.
Isah ya bayyana Manufofi da kudurorinsa da cigaba idan Allah ya bashi damar zama Lamba daya a karamar hukumar, inda yace zai maida hankali akan Mata da Matasa, don ganin rayuwar su ta inganta.
Dattijai Manyan 'Yan siyasa na yankunan sun nuna jin dadin su da tare da tarbar Dantakarar, daga cikin wadanda suka halarci tarukan kuma suka yi kyakkyawar sheda ga Isah sun hada da: Ishaq Tasi'u Modoji, Alhaji Ido Kwado (Sarkin Aikin Sarkin Katsina) Honorable Abdulrahaman, Zaɓaɓɓen Shugaban karamar hukumar Katsina da zai sauka kwanannan Alhaji Aminu Ashiru kofar sauri, Mustafa musa kofar Bai, Alhaji Bishir Dahiru, Alhaji Dikko Bala, da sauran Dimbin Jama'a.
Za a gudanar da zaben kananan hukumomin jahar Katsina a ranar Asabar 15 ga watan February na wannan shekara 2025