Auwal Isah Musa, Katsina Times
A ranar Asabar din nan 1 ga watan Fabrairun 2025, jam'iyyar APC a matakin karamar hukumar Katsina, ta tabbatar tare da ayyana shugaban 'Gafai Charity Foundation' kuma Ko'odinatan 'Dikko Project' wato Dr. Musa Yusuf Gafai a matsayin cikakken dan ja'imyyar APC.
Taron dai ya gudana a Makarantar Gafai Primary School da ke a mazabarsa ta Wakilin Yamma ||, wanda ya samu halartar dattijan yankin, masu ruwa da tsaki a jam'iyyar, 'yantakarkarin Ciyamomi daga wasu kananan hukumomin jihar ta Katsina da sauransu.
Da yake jawabi a matsayinsa na shugaban Dattawan yankin, Tanimu Sada Sa'adu, ya nuna farin cikinsa matuka kan yadda dan nasu ya dawo asalin gidan sa wato jam'iyyar ta APC, bayan da ya tsallake ya bar ta a 'yan shekarun baya, inda ya bayyana hakan a matsayin wajen da ya dace da shi.
Tanimu Sada, ya kuma hore shi da ya ci gaba da shuka ayyukan alherin da aka san shi da shi na taimakon al'umma a fadin jihar, tare da kwadaitar da shi gina yankin da ya fito, duba da shi ne mafarinsa.
Shi ko da yake nasa jawabin, Dr. Musa Gafai, ya bayyana dawowarsa jam'iyyar ta APC a matsayin gane gaskiya, inda ya ce da ma dai kaddara ta sa ya fita daga cikinta, amma yanzu ya dawo gidansa na ainahi.
Da yake bayyana dalilin da ya jawo hankalinsa ya dawo jam'iyyar ta APC, Dr. Gafai, ya ce sakamakon irin ayyukan da gwamna Radda PhD. CON ne ke yi a bangarori da dama a fadin jihar, inda ya bada misali da cewar musamman a bangarorin bangaren Noma, Ilimi, Lafiya, da sauran bangarori.
Bayan kammala gabatar da jawabai daga manyan baki da masu ruwa da tsaki a jam'iyyar da suka halarci taron, an danka masa Katin zama cikakken danjam'iyyar, inda ya rattaba hannu akai.
Wadanda suka halarci taron da gudanar da jawabai a wajen sun hada da: Dantakarar ciyaman na karamar hukumar Bindawa, Honorabul Badaru Musa Giremawa, Dantakarar ciyaman na karamar hukumar Katsina, Honorabul Isah Miqdad A.D Saude da sauransu.
Sauran sun hada da jigon jam'iyyar APC a yanki, Alhaji Ali Kaura, shugaban dattijan wakilin Yamma ||, Tanimu Sada Sa'adu, Shugabar Mata da suka dawo jam'iyyar APC, Hajiya Iya Masanawa, Alhaji Wali Kofar Guga da sauransu.