Afrika Ta Farka, Kuma Ta Cancanci A Zuba Jari A Cikinta, Inji Kashim Shettima
- Katsina City News
- 21 Jan, 2025
- 110
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ne ya bayyana hakan, a yayinda yake gabatar da jawabi wajen taron tattalin arzikin duniya na shekarar 2025 da ke gudana a birnin Davos na kasar Switzerland.
Kashim Shettima ya jaddada cewa Najeriya a shirye take da karɓan kasuwanci da 'yan kasuwa ƙarkashin sabbin dabarun da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samar a kokarinsa na ganin ƙasar ta zama cibiyar zuba jari a Afirka
Shettima ya bayyana yadda ake samun bunƙasar saka hannun jari a ƙasar inda ya roƙi masu zuba jarin da su yi watsi da labaran ƙanzon-kurege da ake yaɗawa kan rashin tsaron dukiyoyin masu zuba Jari a Najeriya
Mataimakin ya ce a yanzu Najeriya na hannun ƙwararru duba da matsayin shugaban ƙasar na gogaggen masani a kan kasuwanci da Mataimakinsa wanda ya share shekaru 20 yana aikin banki,
Mataimakin shugaban ƙasar ya jaddada irin ƙarfin da nahiyar Afirka ke da shi, inda ya bayyana cewa nahiyar ta farka kuma a shirye ta ke ta d
ɗauki matsayinta a duniya yana mai ambato kalaman marigayi shugaban Najeriya, Janar Murtala Mohammed, inda yake cewa Afirka dattijiyar nahiya ce da ba ta cancanci a sanya ta a sahun matasan Nahiyoyi ba.
Jim ƙaɗan bayan kammala tallata Najeriya da Afirka a matsayin wuraren zuba jari, Kashim Shettima ya halarci wani zaman da wasu shuwsgabannin kasashen Afirka da suka haɗa da shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa da shugaban Botswana Duma Boko, zaman na su ya biyo bayan bukatar ƙarfafa dangantakar dake tsakanin ƙasashen Afirka da haɗin gwiwar tattalin arziki.