Shugaban KT-Cares Ya Jaddada Niyyar Taimaka wa Marasa Galihu Tare da Dikko Project Movement
- Katsina City News
- 24 Jan, 2025
- 30
Shugaban shirin bayar da tallafin KT-Cares, Alhaji Nafiu Muhammad, ya tabbatar da aniyarsa ta yin aiki kafada da kafada da kungiyar Dikko Project Movement don gano da tallafa wa marasa galihu a jihar Katsina.
Alhaji Nafiu Muhammad ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar kungiyar ƙarƙashin jagorancin Hon. Musa Gafai a ranar Laraba, 22 ga watan Janairu, 2025.
Shirin KT-Cares, wanda gwamnatin jihar Katsina ta kirkiro tare da haɗin guiwar shirin NG-Cares na gwamnatin tarayya, na da nufin rage radadin talauci da samar da ayyukan yi ga al'umma. Shirin dai ya fara ne tun shekarar 2022, amma a wancan lokacin jihar Katsina ta kasance baya-baya wajen cin moriyar shirin. Sai dai yanzu, saboda jajircewar Gwamna Dikko Raɗɗa, jihar Katsina tana cikin sahun jihohi goma da suka fi cin gajiyar shirin a halin yanzu.
Da yake jawabi, Hon. Musa Gafai ya yi bayanin kudirorin kungiyar Dikko Project Movement da ayyukan da ta sa gaba na taimaka wa al’umma, tare da wayar da kai kan manufofi da tsare-tsaren Gwamna Malam Dikko Raɗɗa, PhD, wanda ke da nufin inganta rayuwar al’ummar jihar Katsina.
A karshe, Hon. Musa Gafai ya gode wa Alhaji Nafiu Muhammad bisa kyakkyawar tarbar da suka samu, tare da tabbatar da shirinsu na aiki tare don ci gaban jihar Katsina.