ILIMI: GWAMNA LAWAL YA AMINCE DA ƊAUKAR MALAMAI 2,000 AIKI A ZAMFARA
- Katsina City News
- 18 Jan, 2025
- 95
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya amince da ɗaukar malamai 2,000 aiki a faɗin jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwar Jihar a ranar Litinin a zauren majalisar gwamnatin jihar da ke Gusau.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa shirin ɗaukar malaman ya zama cika alƙawuran da aka ɗauka a lokacin yaƙin neman zabe.
Sanarwar ta ƙara da cewa, ilimi, kasancewarsa muhimmin bangare na biyu a gwamnatin Gwamna Lawal, ya samu kulawa sosai kuma tuni aka samu sakamakon da ake buƙata.
“Gwamna Dauda Lawal, a ƙoƙarinsa na inganta ilimi a jihar Zamfara, a ranar 14 ga Nuwamba, 2023, ya kafa dokar ta-baci a fannin ilimi a jihar Zamfara.
“Aikin gaggawar da gwamnatin Zamfara ta yi a ƙarƙashin Gwamna Lawal ta haɗa da gine-gine tare da gyara makarantu sama da 400 a fafin ƙananan hukumomi 14 na jihar.
“Samar da tebura masu kujeru biyu ga ɗalibai, wanda ya kai sama da 12,000 a faɗin makarantun da ke ƙananan hukumomi 14 da kuma samar da ingantattun kayan aiki tare da gyara sama da makarantu 400, inda aka saka musu da tebura sama da 700 da kujeru 1,000 na malamai a faɗin ƙananan hukumomin 14. ”
A jawabinsa a wajen taron majalisar, Gwamna Lawal ya ce ɗaukar malaman na daga cikin ayyukan gwamnatinsa a shekarar 2025.
“Gwamnati za ta ɗauki kwararrun malamai 2,000 domin su taimaka wajen ingantawa da kuma farfaɗo da fannin ilimi.
“Ya kamata a ɗauki malamai aiki a matakai don tabbatar da cewa an magance matsalolin da ake samu musamman a makarantunmu ta fannoni daban-daban.
“Ɗaukar ma’aikata wani bangare ne na shirin AGILE da nufin kawo ƙarshen matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta a fannin ilimi da inganta harkar koyarwa ga ɗalibai a makarantunmu a faɗin jihar nan.
“Mun fara ne da ɗaukar malamai 500 aiki a rubu’in farko na wannan shekara. A fagen farko, ya kamata a ba da fifiko ga malamai a fannoni masu muhimmanci kamar Turanci, Lissafi, Chemistry, Physics, Biology, Kwamfuta, da kuma nazarin harkokin kasuwanci."