Yarjejeniyar KYCV da ADUMSAC: Matakin Inganta Koyar da Sana’o’i
- Katsina City News
- 17 Jan, 2025
- 148
Yarjejeniyar KYCV da ADUMSAC: Matakin Inganta Koyar da Sana’o’i
Katsina Youth Craft Village (KYCV) da Aliko Dangote Ultra Modern Skill Acquisition Centre (ADUMSAC) sun kulla wata yarjejeniya ta fahimtar juna (MoU) domin bunkasa koyarwa da horar da matasa a fannoni daban-daban na sana’o’i.
Yarjejeniyar, wacce aka sanya wa hannu a cibiyar ADUMSAC da ke Kano, na da nufin samar da ingantattun kayan aiki da ka’idojin kasa da kasa a fannin koyar da sana’o’i, tare da karfafa gwiwar matasa wajen gudanar da ayyukan ci gaba.
Da yake jawabi yayin rattaba hannu kan yarjejeniyar, Ko’odinetan KYCV na Jiha, Injiniya Kabir Abdullahi Kofar Soro, ya bayyana cewa, “Wannan hadin gwiwa wata babbar dama ce da za ta inganta ayyukan KYCV, tare da tabbatar da daidaituwar cibiyar da manyan ka’idojin duniya wajen bunkasa fasaha.”
Ya kara da cewa wannan tsari ya yi daidai da kudurin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, na kara karfafa matasa ta hanyar samar da dabaru da hanyoyin samun dogaro da kai.
A cewarsa, "Hadin gwiwar zai samar da horo ga ma’aikata da matasan da ke cin gajiyar cibiyar, tare da tallafi daga Hukumar Aikace-aikace da Kula da Fasaha ta Kasa (NBTE). Wannan zai kara tabbatar da ingancin shirin a matakin kasa da kasa."
Shugaban Gudanar da Cibiyar ADUMSAC, Alkasim Hussaini, ya jaddada muhimmancin wannan yarjejeniya, yana mai cewa, “Za mu samar da ƙwarewa, fasaha, da jagoranci wajen tsara manhajoji, samar da kayan aiki, da kula da tsarin horarwa.”
Ya kara da cewa, “Za mu ba da damar amfani da kayan aikin ADUMSAC ga ma’aikatan KYCV da wadanda ke cin gajiyar shirin domin cimma nasarorin da ake bukata.”
Yarjejeniyar ta bayyana a matsayin wata babbar dama ta musayar fasaha tsakanin KYCV da ADUMSAC, tare da kafa ginshikan da za su taimaka wajen kai matasan Jihar Katsina ga matakin gasa a duniya.