Gwamnatin Jihar Katsina za ta Karɓi Baƙuncin Taron ECOWAS na Abinci da Al'adu na Shekarar 2025
- Katsina City News
- 17 Jan, 2025
- 105
Gwamnatin Jihar Katsina za ta karɓi baƙuncin taron ƙungiyar ECOWAS na baje kolin abinci da kuma al'adu na shekarar 2025 mai taken "Darajar Al'adun Afirka da Wadatar Abinci Sabo da Zaman Lafiya da Cigaban Al'umma ".
Mai magana da yawun gwamnan jihar Katsina Ibrahim Kaulaha Mohammed, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ta ce an bayyana jihar Katsina wacce zata karɓi taron a zaman da gwamnan jihar Malam Dikko Umaru Radda PhD, yayi a jiya da wakilan ƙungiyar ECOWAS a fannin wadatar abinci da al'adu (Food Security and Cultural).
Gwamna Raɗɗa ya bayyana jihar Katsina a matsayin ɗaya daga cikin jihohin da ke samar da abinci da wadatar kayan noma, yin hakan zai samar da zaman lafiya da cigaba a yankunan ta.
Ya cigaba da cewa an san jihar Katsina da kara, hakan yasa zamuyi maraba da ƴan uwan mu na cikin gida da sauran baƙi da za su zo daga ƙasashen ECOWAS, al'adun gargajiya da da kuma difilomasiyya zasu taka rawa wajen rage yawan damuwa da haɓɓaka walwala, cigaban al'umma, wadatar abinci, da kuma zaman lafiya.
Gwamnan ya ƙara da cewa shugaban hukumar tarihi da raya al'adu ta jihar Katsina Dakta Kabir Ali Masanawa zai kawo cigaba da sauye-sauye a bukukuwan al'adun da ake a jihar Katsina domin su zama wajen yawon buɗe ido ga mutanen duniya.
Taron abinci da al'adun na ECOWAS yayi daidai da yinƙurin gwamnatin Malam Dikko Umaru Radda, wanda ya sanar a lokacin bikin hawan babbar sallah na sake ƙayata hawan bukukuwan hawan Sallahr da akeyi a faɗin jihar Katsina.
Darakta janar na hukumar ta ECOWAS a fannin abinci, da Bukukuwan Al'adu Ambasada Felix Ihonre, ya bayyana jin daɗin shi a irin tarbar da gwamnan ya yi masu, ya kuma bayyana taron a matsayin abun da zai kawo masu zuba hannun jari a fannin noma daga ciki da wajen ƙasar nan.
Ihonre ya bayyana hukumar raya al'adu ta jihar Katsina a matsayin mazaunin da yayi dai-dai da amsar taron.
Shima da yake magana Dakta Kabir Masanawa, shugaban hukumar Tarihi da raya al'adu ta jihar Katsina, ya bayyana ɗaya daga cikin ribar yin taron a jihar Katsina shine za'a samu ayyukan yi, ƙananan yan kasuwa zasu yi ciniki, da sauran sabbin abubuwa da zasu haɓɓaka tattalin arziki duba da yawan dubban baƙin da zasu halarci taron.
Zaman ya samu halartar Shugaban ma'aikatan gidan gwamnati Hon. Abdulkadir Mamman Nasir, kwamishinar mata Haj. Hadiza Yar’adua, shugaban hukumar bunƙasa hannun jari Alh. Ibrahim Jikamshi, da kuma shugaban hukumar sufuri ta jihar Katsina Alh. Haruna Musa Rugoji.