Tunawa Da Sojoji: Gwamna Lawal Ya Yi Alƙawarin Inganta Rayuwar Iyalan Jaruman Da Suka Rasu
- Katsina City News
- 16 Jan, 2025
- 92
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na inganta jin daɗin iyalan hafsoshi da suka rasa rayukansu a bakin aiki.
Gwamnan ya halarci bikin tunawa da sojojin da suka rasu a ranar Laraba a harabar baje kolin kasuwanci da ke Gusau, babban birnin jihar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta bayyana cewa Gwamna Daudaa Lawal ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 20 ga Rundunar Sojojin Nijeriya, reshen Jihar Zamfara a yayin ƙaddamar da tambarin tunawa da sojojin da suka rasu na shekarar 2025.
Sanarwar ta ƙara da cewa, gwamnan ya duba wani tambari da rundunar sojin Nijeriya suka ɗora. "Gwamna Lawal shi ma ya jagoranci shimfiɗa furannin sannan ya ba da umarnin a yi shiru na minti ɗaya domin karrama jaruman da suka rasu."
A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya jaddada cewa yau ranar tunawa da jaruman da suka mutu ne, kuma kira ne ga ɗaukacin al’ummar jihar Zamfara da ma kasa baki ɗaya.
“Ana yi bikin tunawa da sojojin Nijeriya ne a duk faɗin ƙasar a ranar 15 ga watan Junairu na kowace shekara domin tunawa da kuma jinjina wa waɗanda suka sadaukar da ransu da tsofaffin sojojinmu da suka yi fafutuka wajen kare martabar yankin Nijeriya, waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu domin mu samu damar zama lafiya.
“Muna godiya kuma muna daraja sadaukarwar da suka yi, wanda ya kawo sauyi a rayuwarmu a yau. Tare da godiya da mutuntawa, mun yi alƙawarin ci gaba da tunawa da su tare da tallafa wa iyalan da suka bari.
“Wannan rana ta zama karramawa ga jaruman mu da suka mutu da kuma kira ga ɗaukacin al’ummar jihar Zamfara da ma kasa baki ɗaya. Wata dama ce ta yin tunani a kan sadaukarwar da waɗancan jajirtattun mutane suka yi. Ya kamata sadaukarwar sojojinmu ya zaburar da mu wajen habaka zaman lafiyar da muka samu a yau da kuma fafutukar samar da gobe mai kyau.
“Kada mu manta da muhimmancin tallafa wa iyalan waɗannan jarumai da suka mutu da kuma tsofaffin da suka yi yaƙi domin mu yi barci cikin lumana da kuma waɗanda har yanzu suke da rauni na hidimar da suke yi wa ƙasa. Juriya da sadaukarwarsu dole ne ya tunatar da mu alhakin da ya rataya a wuyanmu na tabbatar da jin daɗinsu. Ta yin haka, muna girmama sadaukarwar da suka yi, kuma muna nuna godiyarmu ga jajircewar da suke yi ga al’ummarmu.”
Gwamnan ya bayyana cewa, duk da ƙarancin kayan aiki, ana samun gagarumin ci gaba wajen magance matsalolin tsaron cikin gida ta jihar ta hanyoyi daban-daban.
"Wannan gwamnatin ba wai kawai ta ba da tallafin kayan aiki masu muhimmanci ba ne. Har ila yau, ta kuma tabbatar da jin daɗin iyalan jami'an da suka rasa rayukansu a bakin aiki. Mun himmatu wajen biyan kuɗaɗen jinya ga waɗanda suka jikkata a ayyukan tsaro da tallafa wa jaruman mu da iyalansu.
“A wani bangare na ƙoƙarin da gwamnatina ke yi na daƙile matsalolin tsaro, mun samar da motocin tsaro sanye da na’urori na zamani, tare da babura ga jami’an tsaro. Wannan yunƙurin na ƙara haɓaka damarsu ta hanyar shiga wurare masu rintsi don tabbatar da cewa babu wani yanki na jiharmu da ke a baya.
"Muna ci gaba da jajircewa wajen ƙarfafa dabarun haɗin gwiwa tare da jihohi makwabta, hukumomin tsaro, da sauran masu ruwa da tsaki don tunkarar ƙalubalen tsaro da ke addabar jiharmu, domin haɗin gwiwa shi ne babban jigon samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali."