Matashin Dan Siyasa Hon. Musa Gafai Ya Ziyarci Shugaban Hukumar Samar Da Ruwan Sha Jihar Katsina
- Katsina City News
- 16 Jan, 2025
- 111
Matashin Dan Siyasa Hon. Musa Gafai Ya Ziyarci Shugaban Hukumar Samar Da Ruwan Sha Jihar Katsina
A kokarin bunkasa dangantaka da lalubo hanyoyin da za su tabbatar da karɓuwar gwamnatin Jihar Katsina, Matashin dan siyasa kuma jigo a jam'iyyar APC, Hon. Musa Yusuf Gafai, ya kai ziyara ga Shugaban Hukumar Samar da Ruwan Sha ta Jihar Katsina, Dr. Tukur Tingilin, a ofishinsa da ke Katsina, a jiya Laraba.
A lokacin jawabin sa, Hon. Musa Yusuf Gafai ya bayyana ziyarar a matsayin wata dama ta ƙarfafa zumunci da yin aiki tare da nufin tabbatar da nasarar Gwamna Malam Dikko Umar Radda wajen gina sabuwar jihar Katsina da kowa zai alfahari da ita. Ya kuma jaddada aniyarsa ta ci gaba da bayar da gudummuwa kamar yadda ya saba tun lokacin yaƙin neman zaɓe.
Shugaban Hukumar Samar da Ruwan Sha, Dr. Tukur Tingilin, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar "Dikko House to House," ya nuna farin cikin sa kan wannan ziyara. Ya tabbatar da kudirinsa na yin aiki tare da Hon. Musa Yusuf Gafai don cimma burin Gwamna Malam Dikko Umar Radda na kawo ci gaba ga al'ummar jihar Katsina.
Ziyarar ta nuna ƙuduri da haɗin kai wajen tallafa wa gwamnatin Jihar Katsina don inganta rayuwar al'umma.