Gwamna Raɗɗa Ya Rantsar da Sabon Kwamishinan Kasafin Kuɗi da Tsare-tsare Alh. Malik Anas
- Katsina City News
- 15 Jan, 2025
- 113
A ranar Laraba 15 ga watan Janairun 2025, Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD,CON, ya rantsar da sabon kwamishinan kasafin kuɗi da tsare-tsare na jihar Katsina Alh. Malik Anas a gidan gwamnatin jihar.
A lokacin da yake jawabi Gwamna Raɗɗa ya bayyana yasan Malik Anas da Jajircewa wajen ayyuka tun lokacin da yake matsayin shugaban ma'aikatan gidan gwamnati a lokacin gwamnatin Alh. Aminu Bello Masari, shi kuma yana babban akawu na jiha.
Riƙe jajurtattun mutane irin Malik wanda suka san aiki, abu ne da zai taimaki wannan gwamnatin tamu, shiyasa lokacin da ya sanar da ni shekarun shi na aiki sun ƙare naga ya kamata ya shigo ciki domin ya bamu gudummuwa.
Kuma yana daga cikin mutanen da suka bamu gudummuwa a lokacin da muke neman wan nan matsayi sabi da haka, bashi muƙamin kamar saka mashi ne da alherin da yayi.
Gwamnan yayi kira ga Malik da ya cigaba a halin shi na taimakon al'umma da ya sani wanda shine silar soyayyar da mutane ke nuna mashi.
Mataimakin gwamnan jihar Katsina Hon. Faruk Lawal Joɓe na daga cikin mutanen da suka halarci wurin sauran sun haɗa da Shugaban ma'aikatan gidan gwamnati Hon. Abdulkadir Mamman Nasir, Sakataren Gwamna Hon. Abdullahi Aliyu Turaji, yan majalisar zartarwa, da sauran ƴan uwa da abokan arziki.