Shugaban jam'iyyar SDP na ƙasa ya baiyana abinda aka tattauna a ganawar sa da El-Rufai
- Katsina City News
- 13 Jan, 2025
- 149
Shugaban jam’iyyar SDP na kasa, Shehu Gabam, ya bayyana sakamakon ganawarsa da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da wasu manyan shugabannin siy
A yayin wata hira da aka yi da shi a gidan Talabijin na Channels, Gabam ya ce sun yi ganawar ne don tattauna halin da kasar ta tsinci kanta a 2024.
Ya kuma ce jam’iyyar ba ta yi wani laifi ba wajen tattaunawa da El-Rufai, wanda dan jam’iyyar APC ne.
Ya ce: “Mun yi ganawar domin duba ga halin da Nijeriya ta tsinci kan ta a 2024 a matsayin jam’iyya. Mu jam’iyyar adawa ce mai zababbun ‘yan majalisa, majalisun jihohi, da kananan hukumomi.
"Me ya sa hakan zai tada kura akan Malam Nasir El-Rufai? Sun ce ba shi da mahimmanci, ba kome ba ne. Me yasa El-Rufai ya dame su? Me yasa ake damuwa da Segun Sowunmi? Idan suna da mahimmanci, me ya sa gwamnati ba za ta ba su muƙamai da suka dace da su don inganta aikin gwamnati ba?, ”in ji shi.