Shugaba Tinubu Ya Haramta Luwadi, Madigo Da Daudu Ga Rundunar Tsaron Najeriya
- Katsina City News
- 12 Jan, 2025
- 113
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan dokar hana luwadi, madigo,
da daudanci tsakanin jami’an sojin Najeriya.
Sabuwar dokar da shugaban ya amince da ita ta kara da haramta wa jami'an tsaron sha ko ta'ammuli da ababen sanya maye a lokacin da suke bakin aiki, kana ta gargade su da su nisanci aiyukan gwalangwaso, da sauya wani bangare na halittar su ta fil-azal, ko yin zanen jiki da ake kira da tatoo a turance.
Wannan dokar na kunshe ne a Sashe na 26 na dokokin aikin Rundunar Sojojin kasar wanda Shugaba Tinubu ya yi wa gyaran fuska a ranar 16 ga Disamba, 2024.
“Neman jinsi ɗaya da sauya halittar Allah ya saba wa dokokin mu da al'adunmu, don haka ba za mu lamunci hakan a rundunar jami'an tsaron kasar mu ba" Inji Shugaba Tinubu.
Shugaban ya ci gaba da cewa:
"Ba zai halatta ga jami'i ko jami'ar tsaron ƙasar mu ya yi ko wace irin hulɗa ta sauya jinsi, ko neman jinsi ɗaya ko ko shiga cikin ayyukan masu wannan ɗabi'a ko kungiyarsu ta duniya da aka fi sani da (LGBTQIA2S+) ko Daudu ba.
“Bai halatta a sami jami’in tsaro a hulɗar rashin ɗa'a da ilahirin jiki ko wani bangarensa ba"
Duk in ji Shugaba Tinubu.
Abinda ake jira a gani shine sabbin hukumce hukumcen ladabtarwar da dokar za ta fitar da zaran an kama wani jami'in tsaro da laifin karya ta.