Taimakon Marayu: Naga Muhimmanci da Tasirin Sa a Rayuwa – Hon. Abdulkadir Nasir Andaji
- Katsina City News
- 08 Jan, 2025
- 117
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Ranar Talata, 7 ga Janairu, 2025, an shirya walimar karramawa ga Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar Katsina a gidan marayu na Atta’awun, Dandagoro.
Taron ya samu halartar manyan malamai irin su Sheik Ahmad Filin Samji da Sheik Yakubu Musa Hassan Katsina, wadanda suka yi jawaban godiya ga shugaban ma’aikatan duba da gudunmawar sa ga marayu.
A jawabinsa, Hon. Abdulkadir Nasir Andaji ya bayyana cewa taimakon marayu yana da tasiri mai girma wajen samun albarka da nasara a rayuwa.
- Ya kara da cewa Allah yana ninka arzikin masu taimakon marayu, kuma hakan yana kara kusancin mutum da Allah.
- Hon. Abdulkadir ya yi kira ga masu hannu da shuni da su kasance masu taimakawa marayu, yana mai cewa taimakon marayu yana kawo rabo mai yawa a duniya da lahira.
- Ya bukaci yara marayu da iyayensu mata dake gidan da su yi addu’o’i ga gwamnatin Jihar Katsina da sauran al’umma domin samun ci gaba.
An shirya Walima mai cike da farin ciki da murna, inda aka gudanar da addu’o’i da kuma bayanai masu karfafa gwiwa. Malamai da shugabanni sun bayyana muhimmancin kula da marayu a matsayin wani bangare na jin kai da addini.
A wajen taron, Sheikh Ahmad Filin Samji ya bayyana cewa taimakon marayu na daga cikin manyan ayyuka da suka cancanci samun lada mai dimbin yawa. Hakazalika, Sheikh Yakubu Musa Hassan ya yaba da irin jajircewar Hon. Abdulkadir wajen tallafawa marayu, yana mai cewa irin wannan kyakkyawan aiki yana kara hadin kai da zaman lafiya a al’umma.
Hon. Abdulkadir Nasir Andaji, wanda aka karrama, ya bayyana cewa taimakon marayu shi ne sirrin nasararsa a rayuwa. Ya ce yana jin dadin yadda taimakonsa ke sauya rayuwar marayu da iyayensu mata, kuma hakan na kara masa kwarin gwiwa na ci gaba da yin kyakkyawan aiki.
Bugu da kari, ya bayyana muhimmancin taimakawa juna musamman ga masu hannu da shuni, yana mai kira da su kasance masu bayarwa domin su amfana a nan duniya da kuma a lahira.
Hon. Abdulkadir ya kuma jaddada bukatar sanya yara marayu cikin kulawa ta musamman domin ganin sun girma cikin kwanciyar hankali da samun ilimi mai amfani.