An kashe kasurgumin ɗan ta’adda, Sani Rusu, a Zamfara
- Katsina City News
- 06 Jan, 2025
- 533
Sojojin Bataliya ta 1 a Arewa Maso Yamma, ƙarƙashin 'Operation Fansan Yamma', sun kashe wani kasurgumin ɗan ta’adda, Sani Rusu, a jihar Zamfara.
Sojojin sun kuma yi nasara a wasu ayyuka daban-daban da suka yi kan ƴan ta’adda a jihar tare da kwato makamai.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da jami'in yaɗa labarai na cibiyar yaɗa labarai ta haɗin gwiwa na Operation Fansan Yamma, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi, ya fitar a Gusau a yau Litinin.
Ya ce “A ranar 4 ga Janairu, sojojin sun gudanar da sintiri zuwa garin Bamamu a ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara, inda su ka yi artabu da ƴan ta’adda a yankin.
“Bayan haka, an kashe wani kasurgumin shugaba a cikin su, Sani Rusu, a yayin wannan artabu.
“Har ila yau, a wannan rana, yayin wani kwanton bauna da aka gudanar bisa sahihan bayanan sirri kan ayyukan ƴan ta’adda a Kwanar Jollof a ƙaramar hukumar Shinkafi, sojojin sun kashe wasu ƴan ta’adda, yayin da wasu su ka sami munanan raunuka.”