Taron Zuriyar Badawa Karo na Biyu a Katsina, An Tattauna kan Tarihi da Makoma
- Katsina City News
- 05 Jan, 2025
- 374
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A ranar Asabar, 5 ga watan Janairu, 2025, aka gudanar da taron zumunci na biyu na zuriyar Badawa a birnin Katsina, wani taro mai muhimmanci wanda ya kasance dandali na tunawa da tarihi da kuma ƙarfafa zumunci tsakanin zuriyar. Wannan taro, wanda aka shirya karkashin jagorancin Alhaji Abu Bazariye, ya haɗa zuriyoyi uku daga Badawa: Zuriyar Turaki Agawa, Zuriyar Gajeren Bade (Marusan Katsina), da Zuriyar Matazu Agawa.
An gudanar da taron a babban ɗakin taro na ma'aikatar kananan hukumomi da ke kan hanyar Kaita, inda ya samu halartar manyan baki, masana tarihi, da masu sharhi kan al'amuran yau da kullum. Wannan ya bawa mahalarta damar tattaunawa mai zurfi kan asalin zuriyar, tarihin shigowarsu Katsina, da rawar da suka taka a cigaban al'umma.
Daya daga cikin muhimman jawaban da aka gabatar shine na Malam Musa Gambo, masani kuma marubucin tarihi daga Zuriyar Turaki Agawa. Malam Musa ya gabatar da kasida mai taken “Tarihin Badawa Katsina (Zuriyar Turaki Agawa),” inda ya yi bayani mai tsawo kan asalin zuriyar, shigowar su Katsina, da yadda masarautar Katsina ta karɓe su da karramawa. Haka nan, ya bayyana rawar wasu fitattun mutane daga zuriyar, tare da haska tarihin su daga Rimin Badawa zuwa Kofar Soro.
Haka kuma, Kamaladdeen Saulawa ya gabatar da kasida mai ƙayatarwa kan asalin Badawa, inda ya yi bayani kan inda suka fito, hanyoyin da suka bi har suka iso Katsina, da irin tasirin su a yankin.
A cikin manyan bakin da suka yi jawabi akwai Farfesa Sani Abdu Fari, shugaban ƙungiyar Dallazawa a jihar Katsina. A jawabinsa, ya yi kira kan muhimmancin ilimi da haɗa auratayya tsakanin ‘ya’yan zuriyar don ƙara ƙarfafa zumunci da haɗin kai. Ya bada misali da zuriyar Dallazawa, inda ya bayyana yadda suka yi amfani da auratayya wajen haɗa dangantaka mai ƙarfi.
Alhaji Ahmed Idi Yemen, wanda ya yi jawabi a madadin zuriyar, ya nuna godiya ga dukkan mahalarta, tare da jan hankalin su kan ƙoƙarin ci gaba da wannan al’ada ta haɗuwa lokaci zuwa lokaci. Manyan bakin da suka halarci taron sun haɗa da Farfesa Sani Abdu, Zaharaddeen Mayanan Safana, Barista Ahamed, Injiniya Abdullahi, da Magaji Allemi, waɗanda dukkansu suka bayar da gudunmawar su wajen tabbatar da nasarar taron.
Badawa suna da tarihin da ya samo asali daga Yobe a ƙasar Borno, inda suka shahara wajen ilimi da mutunci a tsakanin al’umma. Shigowarsu Katsina ya kasance babban abu da ya kawo haɗin kai tsakanin su da masarautar Katsina. Hakan ya sa suka kafa tarihinsu a cikin masarautar, tare da gina dangantaka mai ƙarfi da sauran zuriyoyi irin su Dallazawa da wasu ƙabilu.
Taron ya ƙarfafa muhimmancin tattara tarihi da adana shi ga zuriyoyi masu zuwa. Haka zalika, an cimma matsayar cewa lokaci ya yi da za a kafa gidauniyar tarihi da al’adu na zuriyar Badawa don ci gaba da nuna tasirin su a fagen ilimi da jarimta.
Wannan taro ya kasance wani babban tsani na haɗin kai, ilimi, da zumunta, wanda zai ci gaba da zama ginshiƙin haɗin kan zuriyar Badawa a nan gaba.