Gwamna Abba mutum ne mai amana da tausayi - Kwankwaso ya taya
- Katsina City News
- 05 Jan, 2025
- 130
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023 kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana Gwamna mai ci, Abba Kabir Yusuf, a matsayin mai rikon amana kuma jagora mai tausayi.
Kwankwaso ya yi wannan jawabi ne cikin wata sakon da ya fitar na taya Gwamnan murna a ranar zagayowar ranar haihuwarsa ta shekaru 62.
Ya ce, “Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kafa tarihi a matsayin mai aiki tukuru tun daga lokacin da ya kasance hadimi na, ya zama kwamishina har ya kai matsayin Babban Jami’in gudanarwa na jihar mu.
“A cikin kasa da watanni 19, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauya fuskar Kano ta hanyar kirkirar aikace-aikace da dama da suka shafi bangarori daban-daban na jihar.
“Na musamman a gare ni shi ne jin tausayinsa ga al’ummar Kano da kuma koyaushe yin shawarwari tare da daukar matakai da za su inganta rayuwar Kanawa.
“A cikin shekaru 62 na rayuwarsa, Gwamna Abba ya ba da gudunmuwa mai yawa ga jiharmu, kuma ya tabbatar da kansa a matsayin jigo wajen rikon amana da jagoranci da tausayi.
“Allah Madaukakin Sarki ya ci gaba da yi masa albarka da kara masa karfi da hikima don ci gaba da yi wa al’ummarsa hidima.
Barka da zagayowar ranar haihuwarka, Mai Girma Gwamna.”
Daily Nigeria Hausa