TATSUY: Abotar Biri da Kifi
- Katsina City News
- 02 Jan, 2025
- 154
TATSUY: Abotar Biri da Kifi
Biri ya saba zuwa rafin ruwa domin wanka bayan ya gama yawon cin ’ya’yan itatuwa da tsalle-tsalle har ya gaji. Wata rana, lokacin da ya je wanka, ya gamu da Kifi a cikin ruwa. Sai Kifi ya nemi su kulla abota, Biri kuma ya amince. Suka yi alkawarin cewa za su rike amana tsakaninsu.
Bayan wani lokaci, Biri ya sanar da Kifi cewa zai tafi ganin danginsa a wani daji. Sai Kifi ya shirya masa kayan tsaraba domin tafiyar, suka yi bankwana. Amma bayan tafiyar Biri, sauran kifaye a rafin suka fara guna-guni, suna nuna rashin jin dadin abotarsu da Biri. Hatta wasu daga cikinsu sun yi tayin kashe Kifi ko Biri.
Sai babban kifaye ya ce: "A'a, ba maganar kisa. Kisan kai zai haifar da gaba tsakaninmu da birai." Don haka, suka yanke shawarar cewa za su yi wa Kifi tayin sarauta a matsayin hanyar kawo karshen abotarsa da Biri. Suka kira Kifi, suka ce masa idan yana son sarauta, sai ya kawo zuciyar Biri.
Da Kifi ya ji haka, sai ya ce musu: "Mun yi alkawari da Biri cewa ba za mu ci amanar juna ba. Ba zan iya cin mutuncinsa don samun sarauta ba." Duk da haka, sai ya amince ya tattauna da Biri a kan lamarin.
Bayan dawowar Biri daga tafiya, sai ya kai wa Kifi ziyara kamar yadda ya saba. Suka yi gaisuwa da hira, sannan Kifi ya bayyana masa abin da ya faru. Ya ce an ce masa idan har zai kawo zuciyar Biri, za a ba shi sarauta.
Biri ya yi kamar ya amince, ya ce: "Ba matsala, amma ka san bana yawo da zuciyata. Tana rataye a kan bishiya. Bari in dauko maka ita."
Sai Kifi ya raka shi har bakin ruwa. Da Biri ya hau bishiya, sai ya ce da Kifi: "Daga yau ba zan sake abokantaka da kai ba. Kuma ba zan sake shiga ruwa ba."
Shi ya sa har yau birai ke tsoron shiga ruwa saboda wannan dabara ta Biri.
Darasin da labarin yake koyarwa:
1. Hassada ga mai rabo taki ce.
2. Dabara kashin kwance.
3. Ka rike amana da gaskiya a ko da yaushe.
4. Kafin ka yaudari wani, ka tabbatar ba zai fahimci dabararka ba.
5. Duk wanda ya kulla abota, ya kamata ya kula da martabarta.
TASKAR TATSUNIYOYI NA DAKTA BUKAR USMAN