An Kaddamar Da Littafi Mai Bayyana Nasarorin Da Gwamman Jihar Katsina Ya Cimmawa A Bangaren Bungasa Ilimi Mai Zurfi.
- Katsina City News
- 29 Dec, 2024
- 150
Daga Auwal Isah Musa.
Mai taimaka wa gwamnan jihar Katsina kan kafofin sadarwa na zamani a ma'aikatar Ilimi mai zurfi, Fasaha da Koyon Sana'o'i, Honorabul Usman Abubakar Danmusa, ya shirya taron gabatar da littafin nasarorin da gwamnan jihar ta Katsina, Dr. Dikko Umar Radda Ph.d ya cimmawa a ma'aikatar daga a cikin watanni 18 na kama Mulkin jihar.
Taron wanda Ma'aikatar ta dauki nauyin gudanarwa mai taken "Illuminating a path with glory in higher, technical and vocational education" a turance, an gudanar da shi a ranar Lahadin nan a dakin taro na Katsina Motel.
Da yake jawabi, Mawallafin Littafin, Honorabul Usman Abubakar Danmusa, ya bayyana irin ayyukan da gwamnan ya aiwatar a Ma'aikatar cikin kasa da shekaru biyu na kasancewarsa gwamnan jihar.
Honorabul Danmusa, ya bayyana ayyukan gwamnan a matsayin abin da ya zamar masa wajibi ya rubuta su a littafi ya taskace don tasowa su gani kuma su yi koyi, kuma su shaida irin ayyukan da gwamnan jihar ya yi wajen bunkasa Ilimi don goben al'umma a lokacin mulkinsa.
Da yake tsokaci game da Littafin da aka wallafa, a matsayinsa na babban bako mai jawabi a wajen, Dr. Bashir Usman Ruwan Godiya, ya bayyana irin yadda aka nuna kwarewa tun a wajen rubuta littafi ta hanyar bin ka'ida, sannan ya bayyana ayyukan da aka zayyano cewar gwamnan ya yi a cikin littafin a matsayin na gaske ba shaci fadi ba.
Dr. Ruwan godiya, ya kuma yi tsakure na irin ayyukan gwamnatocin baya na jihar suka yi don ci gaban jihar musamman a bangaren Ilimi, tun daga Marigayi Alhaji Umaru Musa, Dr. Ibrahim Shema, Honorabul Aminu Bello Masari zuwa ga Dr. Dikko Radda, inda ya bayyana ayyukan gwamna Radda a matsayin fadadawa daga na wadancan na baya.
Shi ko a jawabinsa, Kwamishinan ma'aikatar Ilimi mai zurfi, Honorabul Isah Muhammad Musa, ya yaba wa Matashin kan iya aikin da aka kawo shi ya yi a ma'aikatar, tare da shan alwashin ci gaba da ba shi dukkan goyon baya wajen fitowa da sanar da al'ummar jihar irin ayyukan bunkasa Ilimi da gwamnan ke yi musamman a bangaren Ilimi mai zurfi babu kama hannun yaro.
Shugabannin rukunin manyan makarantu a Jihar ta katsina wadanda suka halarci taron da suka hada da: Jami'ar Umaru Musa 'yaradua, Kwalejin Kimiyya da Fasa ta Isah Kaita da ke Dutsinma, Kwalejin Fasaha da Kere-kere, Kwalejin Koyar da Shari'a da Ilimin Addinin Musulunci, da Kwalejin kimiyya da Fasaha ta Hasan Usman Katsina sun gudanar da jawabin irin nasarorin da makarantun nasu suka samu a karkashin mulkin gwamnan, daga hawansa zuwa yanzu.
Wadanda suka halarci taron sun hada Shugaban Ma'aikatar raya karkara da ci gaban jama'a, Farfesa Abdulhamid Ahmad, Shugaban Jami'ar Umaru Musa 'Yar'adua Farfesa Salihu Muhammad, Shugaban Kwalijin Ilimi ta Isah Kaita da ke Dutsin-ma, Dr. Samaila Futuwa, Kwamishiniyar Ma'aikatar Ilimi a matakin farko da Sakandare Zainab Musa Musawa wadda ta samu wakilcin Shugabar riko ta Kwalejin Fasha da Kere-kere Dr. Hindatu Salisu Abubakar, Shugaban Kwalejin Ilimin Shari'a da addinin Musulunci ta Yusuf Bala Usman Dr. Abdulmutallib Ahmad, tsohon mai ba gwamnan shawara kan Ilimi mai zurfi Dr. Bashir Ruwan Godiya, Shugaban Kwalejin kimiyya da fasa ta hassan Usman Katsina Polytechnic Dr. Aminu Kalloh Doro wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Wakilin Majalissar Sarki, Daraktoci da sauransu.
Sauran sun hada da Malam Muhammad Marwan, Alhaji Bala Dikko Kofar Sauri, Alhaji Abubakar 'Yantumaki da suransu.