Gamayyar Kungiyoyin APC Sun Nuna Gamsuwarsu da Gudunmawar Musa Gafai
- Katsina City News
- 24 Dec, 2024
- 191
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Gamayyar kungiyoyin jam’iyyar APC masu goyon bayan gwamnatin Gwamna Dikko Umaru Radda a jihar Katsina sun bayyana godiyarsu ga tsohon dan takarar kujerar majalisar tarayya daga mazabar Katsina, Alhaji Musa Yusuf Gafai, bisa goyon bayan da yake bai wa jam’iyyar da kuma gwamnatin mai ci a jihar.
An bayyana hakan ne a wata ganawa ta musamman da aka gudanar ranar Talata, 24 ga watan Disamba 2024, a ofishin Muhammad Wali Kofar Guga, wanda ke kusa da Filin Wasa na Muhammadu Dikko, a Katsina. Taron ya samu halartar shugabannin gamayyar kungiyoyin, mambobi, da manema labarai, inda suka yaba da rawar da Musa Yusuf Gafai ke takawa wajen tallafa wa gwamnatin Dikko Radda.
Da yake magana a madadin gamayyar kungiyoyin, Alhaji Wali Kofar Guga ya bayyana Musa Gafai a matsayin mutumin kirki da ke da dimbin basira da kwarewa wajen taimakawa gwamnatin jihar Katsina ta samu nasara. Ya ce, “Musa Yusuf Gafai ya kasance ginshiƙin cigaban jam’iyyar APC a jihar Katsina. A matsayinmu na mambobi masu goyon bayan gwamnati, mun yi kira gareshi da ya dawo cikin jam’iyyar, kuma cikin ikon Allah ya amsa kiranmu. Wannan mataki yana kara tabbatar da cewa shi da Gwamna Dikko kamar *A da B* ne a wajen ganin jihar Katsina ta cigaba.”
Alhaji Wali ya kara da cewa, “Malam Dikko Radda jajirtaccen gwamna ne wanda babu kamarsa a yankin Arewa. Muna alfahari da irin nasarorin da yake samu, musamman a bangaren raya birane da ci gaban al’umma. Wannan shi ne dalilin da ya sa muka ga dacewar yin kira ga masu ruwa da tsaki kamar Musa Yusuf Gafai don su ci gaba da mara baya ga wannan gwamnati mai nasara.”
A yayin taron, Alhaji Wali ya yaba wa Gwamna Dikko Radda bisa kammala ayyukan titin Kofar Guga zuwa Kofar Soro, wanda ya ce ya kawo gagarumin cigaba ga birnin Katsina. “Mun fi kowa farin ciki da wannan aiki na alheri, domin wannan titi na daya daga cikin abubuwan da muka dade muna fata tun zamanin mulkin soja,” in ji shi.
A karshe, gamayyar kungiyoyin sun bayyana godiyarsu ga Gwamna Dikko Umaru Radda da Alhaji Musa Yusuf Gafai bisa jajircewarsu wajen ganin jihar Katsina ta samu cigaba mai dorewa, tare da yin kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da goyon bayan gwamnatin jihar don tabbatar da nasarorin da aka fara samu.