YAKIN KATSINA DA MARADI.
- Katsina City News
- 24 Dec, 2024
- 199
Yakin Katsina da Maradi yana da nasaba da Jihadin Shehu Usman Danfodio na Karni na sha tara. Acikin shekarar 1804, Shehu Danfodio ya samu nasarar Jihadi a Kasar Hausa inda ya kafa Daular Sokoto( Sokoto Chaliphate). A Katsina Mujahidai ukku ne Shehu Usman Danfodio yaba Tutar Kaddamar da Jihadi a Katsina. Wadannan Mujahidai sune Malam Ummarun Dallaje, Wanda ya fito daga Zuriar Fulani Dallazawa, Malam Ummarun Dunyawa, Wanda ya fito daga Fulani Sullubawa, sai Malam Muhammad Na Alhaji Wanda ya fito daga zuriar Fulani Yandakawa. Shi Malam na Alhaji shi yaci Kasashen yamma maso Gabas na Katsina da da Yandaka, Ruma, Zakka, Danmusa, da sauransu. Shi kuma Ummarun Dunyawa yafi karfi a shiyyar Maradi wajajen Zandam, saboda haka, a wadannan wuraren ne ya kaddamar da Jihadin sa, yaci Kasashen da suka hada da Kaita, Kusa, da sauransu. Shi Kuma Ummarun Dallaje ya gudanar da Jihadin shi a mafi yawancin Kasashen dake cikin birnin Katsina. Bayan an Kare Jihadi, an zabi Ummarun Dallaje ya Zama Sarkin Katsina.
YAKIN KATSINA DA MARADI.
Kamin Jihadin Shehu Usman Danfodio na Karni na (19) Maradi tana karkashin ikon Kasar Katsina, Kuma Sarkin Katsina Yana da Wakili na dindindin a Maradi tun wajen tsakiyar Karni na sha Bakwai. Bayan da aka Kare Jihadi a Katsina sai aka Kasa Kasa Katsina gida ukku ga shugabannin Jihadi, Kuma kowa baya shiga cikin Kasar kowa a tsakanin su. Shi Ummarun Dunyawa (.Sarkin Sullubawa) shi ke kula da shiyyar Maradi, da sauran Garuruwan dake kusa da Maradin kamar Tasawa, da Gazawa da sauransu. To sai wani lokaci ya tura Wakilin shi Mai kula da Maradi akan ya anso mashi Haraji, to su Kuma Maradawa sun gashi da mulkin da yake masu, da yazo Maradin sai suka kashe Wakilin Katsina, Mai suna Mani Asha, sannan Kuma Sarakunan Habe wadanda Yan Jihadi suka Kora daga Katsina a lokacin Jihadi, suka gudu suka koma Damagaram da Zama,a matsayin Yan gudun Hijira, sai Maradawa suka aika masu cewa su dawo Maradi su ci gaba da mulki a Maradin, domin sun kashe Wakilin Katsina kuma sun maida Maradi Mai cin gashin kanta, sun ware daga Katsina. To sai su Sarakunan Habe na Gidan Korau dake Damagaram suka taso suka dawo Maradi, suka kafa wata sabuwar Masarautar su, wadda suka Kira da Sarkin Katsina Maradi. Wannan shine asalin Sarautar Sarkin Katsina, Wanda ya Fara daga Dankasawa acikin shekarar 1816. To Kuma su Haben sai suka ci gaba da kawo hari a Katsina da niyyar su kwaci mulkin su daga hannun Fulani Dallazawa, Yakin ya faro ne daga shiyyar shi Sarkin Sullubawa Ummarun Dunyawa, a inda suka mamaye Garuruwan Tasawa, da Gazawa, da sauransu, suka koma karkashin Maradi, Wanda kamin lokacin duk Kasashen Katsina. Sun Kuma kawo hare hare a shiyyar Batsari, da Ruma da Dajin Rugu. Tarihi ya nuna Yakin Katsina da Maradi ya dauki tsawon lokaci ana yin shi. Dalilin dadwawar Yakin shine rabuwar da Katsina gida ukku ga Shuwagabanin Jihadi, kowa Kuma Bai shiga hudda kowa. Ance Sarakunan Habe dake Maradi, sun ta kawo a Katsina da niyyar su kwaci mulkin su daga hannun Fulani Dallazawa tun daga shekarar 1816, basu daina kawo harin sai zuwan Turawa Katsina acikin shekarar 1903.
Alh. Musa Gambo Kofar soro