Rudani: Tinubu ya naɗa shugabanni biyu ga hukuma daya
- Katsina City News
- 20 Dec, 2024
- 204
An samu rudani kan naɗin shugabanni biyu masu rike da mukamin Manaja Darakta/ Babban Jami’i na Hukumar Raya Kogin Niger (UNRBDA).
Kasa da watanni biyu bayan da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya naɗa Aliyu Tajudeen, ƙani ga Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, a matsayin Manaja Darakta kuma Babban Jami’i na hukumar, shugaban ƙasar ya sake naɗa wani shugaban, Dangajere Jaja, wanda Gwamna Uba Sani ya bada sunansa.
Rahotannin DAILY NIGERIAN sun nuna cewa Kakakin Majalisar ya yiwa "Gwamnan wayo” ta hanyar samun amincewar shugaban ƙasa domin ɗan uwansa, a lokacin da aka ce wanda Gwamna Sani ya bayar yana kan “matakin tantancewa.”
Cikin ɓacin rai kan wannan “ƙarfin hali” na Kakakin Majalisar, gwamnan ya sake ganawa da shugaban ƙasa tare da samun amincewa domin wanda ya bada sunansa, Dangajere Jaja.
Rahotannin DAILY NIGERIAN sun nuna cewa naɗin Mista Tajudeen an sanar da shi a cikin wata wasiƙa mai kwanan watan 30 ga Oktoba, 2024, wacce Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya rattaba wa hannu.
Sai dai, abin mamaki ya kasance a yayin da Shugaba Tinubu ya sake sanar da naɗin Mista Jaja a matsayin Manaja Darakta na wannan hukuma guda.
Sanarwar naɗin Mista Jaja, wacce ba ta yi magana kan Mista Tajudeen ba, an bayyana ta ne cikin wata sanarwa da Mataimakin Shugaban Ƙasa kan yada Labarai Bayo Onanuga, ya fitar.