Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima Ya Wakilci Shugaba Tinubu a Taron Ƙaddamar da Babban Jirgin FPSO a Dubai
- Katsina City News
- 14 Dec, 2024
- 168
Katsina Times
A yau, mataimakin shugaban ƙasa, Malam Kashim Shettima, ya wakilci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a wajen taron ƙaddamar da kuma sanya suna ga babban jirgin Floating Production, Storage, and Offloading (FPSO) mai darajar dala miliyan 315 a tashar jiragen ruwa ta Drydocks World Dubai, da ke Ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa.
Wannan ci gaba na daga cikin manyan nasarorin da aka cimma sakamakon gyare-gyaren da Shugaba Tinubu ya kawo a ɓangaren harkar mai, musamman wajen ƙara ƙarfin haƙar man fetur a Nijeriya.
Babban jirgin FPSO yana da ƙarfin ajiyar ganga miliyan ɗaya na man fetur, kuma za ya fara da haƙar ganga 17,000 a kowace rana, wanda ake sa ran zai ƙaru zuwa ganga 30,000 a kowace rana. An tsara cewa za a kawo jirgin zuwa Nijeriya a farkon zangon shekarar 2025, sannan za ta fara aiki a tashar man fetur na Okwok cikin farkon rabin shekara.
Wannan sabuwar cibiyar tana da ma’ana fiye da kasancewa wani aikin gine-gine na ruwa kawai. Tana zama hujjar nasarar gyare-gyaren da Shugaba Tinubu ya aiwatar a ɓangaren man fetur, tare da nuna ƙaruwar tasirin Nijeriya a idon duniya.
Hoto: Mataimakin Shugaban Ƙasa.