Gwamna na Jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya Kirkiri Masarauta ya Naɗa Mahaifinsa da Ya Auri Mata 30
- Katsina City News
- 10 Dec, 2024
- 272
Katsina Times
Gwamnan Jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya tabbatar da kafa masarauta ta musamman ga mahaifinsa wanda ya taɓa auren mata sama da 30. Daga cikin matan, 13 sun bar gidan, yayin da saura 17 ke nan a yanzu, tare da haifar yara 108, ciki har da Gwamnan na yanzu na Jihar Ebonyi.
Gwamna Nwifuru ya umarci Majalisar Dokoki ta Jihar Ebonyi da ta ƙirƙiro sabuwar masarauta, kuma sun amince da hakan tare da naɗa mahaifinsa a matsayin sarkin.
A makon da ya gabata, gwamnan ya mika sandar mulki ga mahaifinsa a matsayin sarki wanda gwamnati ta amince da shi, yayin da aka yi bikin sarautar a karshen makon da ya gabata, inda manyan mutane suka halarta, ciki har da H.E Mike Elechi, H.E David Umahi da wasu fitattun mutane daga jihar.
A yayin bikin sarautar mahaifinsa a matsayin sarkin al’ummar "Oferekpe Agbaja" mai cin gashin kanta, Gwamna Nwifuru ya bayyana cewa mahaifinsa ya taɓa mallakar mata sama da 30 a baya. Duk da haka, wasu daga cikin matan sun bar gidan saboda rashin haihuwa, wanda hakan ya rage adadin matan zuwa 19 a wani lokaci. A yanzu, mahaifinsa na da mata 17 da kuma yara 108, wanda cikin su akwai digiri 21 daga jami’o’i, har da gwamnan kansa.
Duk abin da za ka ce, yara 108 daga mutum ɗaya suna da yawa sosai. Wannan iyali lallai ya cancanci samun masarautar kansu.