TARIHIN UNGUWAR RIMIN BADAWA KATSINA.
- Katsina City News
- 08 Dec, 2024
- 372
Unguwar Rimin Badawa tana gabacin Tudun wada. Daga kudu tayi iyaka da Kofar Durbi, daga Arewa ta yi iyaka da iyatanci. Daga gabas ta yi iyaka da Filin Samji. An kafa wannan Unguwa a lokacin Mulkin Sarkin Katsina Ummarun Dallaje(1807-1835). Mutane da suka kafata sune Badawa, wato mutanen Bade dake Jihar Yobe ta yanzu.
A Kasar Bade dake Gashua, cikin Jihar Yobe ta yanzu, suna da wata al'ada wadda a duk karshen Shekara suna taruwa su tattauna al'amurransu na yau da kullum, misali idan anyi rasuwa a cikin shekarar to ba zaayi bikin Mutuwar ba sai shekara ta zagayo an hadu a wajen wannan taron, hakanan bikin daurin aure duk a cikin wannan lokacin akeyin shi, idan kaka tayi an samu amfanin noma. To ana cikin wannan hali sai suka rutso da lokacin Jihadi. Ana Jihadi a Sokoto na Shehu Usman Danfodio, a Borno Kuma Shehu Elkanemi shima ya Fara nashi Jihadin. To sai Badawa sukayi shawarar cewa ga Jihadi yazo, Ina zamu tafi muyi mubayaa, Shuwagabanin ukku daga cikin su sukayi rinjaye. Daga cikinsu akwai 1. Sarkin Gorgaram Lawan Babuje, 2. Sarkin Katamma Dugun Zanaske, 3. Sai Sarkin Gunje Mai Makama. Sai wadannan Sarakunan Ukku suka tafi Borno, sukayi mubaya'a wurin Shehu Elkanemi, yace masu to tunda kun kawo kanku ba zamu yake ku ba, amma zaku rinka biyan ( Haraji) Jiziya ta bayi maza da mata kowace shekara. Suka ce sun yarda akayi Sulhu akan haka. Amma da suka dawo gida Bade, sai Lawan Babuje Sarkin Gorgaram da Dugun Zanaske Sarkin Katamma suka ce harajin yayi masu yawa, zasu iya badashi sau daya kawai, amma bazasu iya badashi fiye da sau daya ba, suka warware sulhun da sukayi tsakanin su da Borno. Shi kuwa Mai Makama Sarkin Gunje yace shi dai bai goyi bayan wannan shawara ba, sabo da haka ya koma Borno ya sanar da Elkanemi. Yaci gaba da Zama tare da Shehu Laminu( Elkanemi) saboda yasan cewa idan ya dawo Bade zasu kashe shi. Sarakunan Bade suka gina Ganuwar Gorgaram, saboda sun San cewa Shehun Borno zai kawo masu hari akan warware akaqawarin da sukayi, Kuma idan harin yayi nasara zaa iya dora Mai Makama akan su, ya Zama shugabansu. Tunanin su yayi amfani tunda Borno ta kawo masu hari har so biyu amma batayi nasara akansu ba. Shi kuwa Mai Makama a Borno ya mutu wani kauye kusa da Birnin Ngazargamu, bai sake dawowa Bade ba. Zuruar Lawan Babuje ana kiransu Gid-gid Kuma da harshen Turanci ana kiransu Gid-gid Dynasty, sune ke Sarautar Bade har zuwa yanzu.
Shi kuwa Muhammadu Dogo Wanda suka fi sani da Agawa a Bade ya mutu Sokoto wurin Sarkin Musulmi Muhammad Bello a wajen shekarar 1821, tare da mabiyan shi da gaba dayan dangin shi. Ya samu Sarkin Musulmi Muhammad Bello a wajen shekarar 1821, domin Shehu Danfodio ya rasu a shekarar 1817. Yace ma Sarkin Musulmi yazo ne da niyyar ya amshi tuta ta Jihadi domin ya kaddamar da Jihadin Musulunchi a Kasar Bade, sai Sarkin Musulmi Bello yace mashi bazan baka takarda ka Yaki mutanen Bade, domin Buhari Sarkin Hadejia yayi Mamu Tawaye mutanen Bade suka taimaka mamu muka kashe shi, Kuma munyi yarjejenjya da Shehu Elkanemi cewa a tsakaita yaki a tsakanin wadannan Kasashen. Sarkin Musulmi yace mashi amma zan baka takarda zuwa Katsina wajen wani Almajirin mu( Malam Ummmarun Dallaje) kuje ku taimaka mashi Yaki da Sarakunan Habe da suka koma Maradi da Zama. Wannan shine dalilin zuwan BADAWA zuruar Turaki Agawa Katsina acikin shekarar 1821.
Da Badawan suka zo Katsina, sun Fara zama a dai dai Unguwar Rimin Badawa, wadda yanzu take kusa da Filin Samji Katsina. Ance a jikin Sirdin Dawakansu akwai yayan Rimi, sai wannan Rimin ya zuba a dai dai wurin da suka Fara Zama, sai itacen Rimi suka fito, sai mutane suka rika cema wurin Rimin Badawa. Ta hakane Unguwar Rimin Badawa ta kafu a Katsina. Bayan Badawa sun zauna a wurin sai suka kafa Gonakinsu da Gidajensu a wurin. Daga baya wurin ya Zama wata babbar Makabarta wadda ake binne mutane. Mutum na farko da aka Fara rufewa a Makabarta shine Jagoran BADAWA Muhammadu Dogo acikin shekarar 1833.
Daga baya sai Badawan suka tashi daga Unguwar Rimin Badawa suka koma cikin gida Kofar
Soro da Zama. Dalilin dawowar Badawa a Kofar soro shine Muhammadu Agawa daya daga cikin Jagororin Sarautar Turaki, wadda Sarkin Katsina Muhammadu Bello ya nadashi acikin shekarar 1861. Sai Sarkin Katsina ya umarce shi da ya dawo Kofar soro da zama, domin aikin Turaki na dare da rana ne baya da kayyadaden lokaci. Turaki Agawa yabi umarni da Sarki ya bashi ya taso daga Rimin Badawa ya dawo Kofar soro da zama da gaba dayan Dangin shi da bayin shi da Barorin shi. Sunzo Kofar soro tare da Magayaki Mamman Gajeran Bade, Wanda ya zauna a Unguwar Kuka, shine Zuruar ke rike da Sarautar Marusan Katsina a Dutsi a halin yanzu.
Wasu daga cikin Badawa Zuruar Turaki Agawa sun hada:.
1. Late Alhaji Mamman Dawai Katsina ( Retire Permanent Secretary Kaduna State Ministry for Local Government and chieftancy Affairs)
2. Late Alhaji Abu Yaro ( First Account General Katsina State.
3. Alhaji Abu Bazariye ( Chairman Teachers Registration Council of Nigeria ).
4. Alhaji Ibrahim Sayyadi ( Former Secretary to the Katsina State Government).
5. Alhaji Aminu Abdullahi ( Barayan Katsina and Deputy Commandant General Nigerian Security and Civil Depence Corps Rtd).
6. Dr. Mustapha Abu Yaro ( Executive Director National Eye Centre Kaduna).
7. Barrister Ahmed Abdu ( Former Cleak Katsina State House of Assembly and Former Director Federal government/ Barayan Bade. ).
8. Engineer Iro Gambo( Former Director Voter Registry Department INEC HQS ABUJA).
9. Alhaji Yusuf Gambo Kofar soro ( Former Director of Local Government Administration)
10. Justice Aminu Tukur Kofar Bai ( High Court Judge).
11. Alh. Musa Gambo Kofar soro( Chief Admin Officer INEC Kano office and Autho of Book entitle A History of Badawa in Katsina. Da sauransu.
Alh. Musa Gambo Kofar Soro.