Mamaye Fadar Sarkin Kano Hakan na iya Kawo Rashin Zaman Lafiya a Kano -Gwamnatin Jihar Kano
- Katsina City News
- 06 Dec, 2024
- 204
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana rashin jin daɗinta game da matakin hukumomin tsaro na mamaye Fadar Mai Martaba Sarkin Kano.
A wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Dr. Abdullahi Baffa Bichi, ya ce wannan matakin ba wai kawai ya janyo damuwa ba, har ma yana iya yin barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
Gwamnatin ta yi kira ga hukumomin tsaro su rungumi aiki cikin gaskiya da adalci, tare da mutunta dokokin kasa da al’adun gargajiya. Haka kuma, ta yi kira ga jama’a su ci gaba da kwantar da hankalinsu da bin doka a kowane lokaci.
Sanarwar ta nuna aniyar gwamnatin Kano na tabbatar da zaman lafiya da martabar masarautu, domin ci gaba mai dorewa.