NLC Ta Bukaci Jihohi da Ba Su Fara Biyan Sabon Albashi Na Ƙasa Ba Su Gaggauta Aiwatarwa
- Katsina City News
- 29 Nov, 2024
- 184
Zaharaddeen Ishaq Abubakar (Katsina Times)
Hedikwatar Ƙungiyar Ma'aikatan Najeriya (NLC) ta yi kira ga jihohin da har yanzu ba su fara aiwatar da tsarin sabon mafi ƙanƙancin albashi na ƙasa ba, su gaggauta daukar matakin da ya dace. Wannan kiran ya biyo bayan shawarar Majalisar Gudanarwa ta Ƙasa (NEC) da Kwamitin gudanarwa na Ƙasa (CWC), wanda suka bayar da umarni na aiwatarwa kafin ƙarshen watan Nuwamba 2024.
A cikin wata wasika mai ɗauke da sa hannun Sakatare Janar na NLC, Emmanuel Ugboaja, da aka fitar ranar 29 ga Nuwamba 2024, ƙungiyar ta bayyana cewa wasu jihohin, ciki har da Abia, Akwa Ibom, Ebonyi, Ekiti, Enugu, Babban Birnin Tarayya (FCT), Imo, Nasarawa, Kaduna, Katsina, Oyo, Sokoto, Yobe, da Zamfara, ba su fara biyan sabon albashin ba. An bayyana cewa ma’aikata a jihohin suna ci gaba da karɓar albashi bisa tsohon tsari ba tare da wata takamaiman rana na fara aiwatar da sabon tsarin ba.
Wasikar ta jaddada bukatar shugabannin ƙungiyar a matakin jihohi su yi aiki da matakin da NEC da CWC suka bayar don tilastawa jihohin aiwatar da sabon tsarin albashi. NLC ta nemi a aika kwafin wasiƙun zuwa ga hedikwatarta don tabbatar da daidaito wajen tsare-tsaren tursasawa.
A ƙarshe, ƙungiyar ta bayyana godiyarta tare da nanata taken ta na “Rauni ga Daya Rauni ga Duka,” tare da kira da a yi da gaske wajen tabbatar da ganin jihohin sun fara biyan sabon albashi.