Dan Majalisar Katsina, Hon. Sani Danlami, Ya Kaddamar da Muhimmin Aikin Titin A karamar hukumarsa
- Katsina City News
- 13 Nov, 2024
- 251
Zaharaddeen Ishaq Abubakar (Katsina Times)
Dan majalisar tarayya mai wakiltar Katsina, Hon. Sani Aliyu Danlami, ya kaddamar da aikin titin kilomita biyu mai hade Gidan Dawa da Masallacin GRA. Taron ya samu halartar manyan baki daga cikin gari, da suka hada da shugabannin yankin, malaman addini, da wakilan al'umma.
A cikin jawabinsa, Hon. Danlami ya bayyana cewa wannan aikin titin wani bangare ne na alkawuran da ya dauka ga al’umma lokacin kamfen. Ya kara da cewa, akwai sauran manyan tituna guda hudu da yake shirin ginawa a Katsina, ciki har da wadanda za su ratsa yankin ofishin Kwastam, Fadar Gwamnati, da Shehu Dr. Matazu road layout.
Baya ga gyaran tituna, Hon. Danlami ya kuma bayyana wasu muhimman ayyuka da suka hada da cibiyar kiwon lafiya a Shinkafi B, azuzuwa guda shida a makarantar firamare ta Sani Danlami, da wasu ayyuka a manyan makarantun sakandare da cibiyoyin kiwon lafiya.
Shugabannin yankin sun yaba wa Hon. Danlami bisa wannan gagarumin kokari, tare da jaddada sadaukarwarsa wajen inganta ababen more rayuwa da jin dadin al'umma.